Sauran Kiris mu kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Sauran Kiris mu kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Gwamnatin Tarayya

A daren ranar Alhamis din da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake bayar da tabbaci tare da jaddada matsayarsa kan cewa sauran kiris gwamnatin tarayya ta kawo karshen ta'ddancin Boko Haram a kasar nan ta Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, shugaba Buhari ya yiwa al'ummar Najeriya albishir tare da shan alwashi na cewar sauran kiris ta'addancin Boko Haram ya zamto tarihi a kasar nan.

Shugaban Buhari ya yi wannan albishir yayin da ya karrama jaruman fina-finan hausa na Kannywood da wata liyafar dare a fadarsa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Sauran Kiris mu kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Buhari
Sauran Kiris mu kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Najeriya - Buhari
Asali: Facebook

Yake cewa, ba bu duk wata kungiya da za ta buya karkashin rigar addini da manufa ta kawo barazana ta tashin-tashina da dimauta zukatan al'ummar kasar nan da za ta samu sukuni a karkashin gwamnatin sa.

Buhari wanda ya yi kalamansa cikin harshen Hausa ya bayyana cewa, akwai kaucewa hanyar gaskiya cikin zubar da jinin al'umma a wuraren Ibada ko kuma Kasuwanni ga duk wanda yayi imani da Ubangijin sa.

KARANTA KUMA: Hukumar NIA tayi gargadi kan wani Magani mai dauke da Tsokar 'Dan Adam da zai shigo Najeriya daga Kasar China

Yake cewa, ba bu dace ga duk mai imani ya rinka karaji da kururuwa ta Allahu Akbar yayin da yake zubar da jinin al'umma da salwantar ma su da dukiya."

Ya ci gaba da cewa'"Dayan biyu ne, ko dai ba ka da masaniyar abinda kake furtawa ko kuma ba ka yi imani da Ubangiji ba. Saboda Ubangiji ya haramtawa kansa Zalunci kuma ya tsarkaka daga rashin adalci."

A yayin haka shugaban kasar ya nemi jaruman na wasan kwaikwayo akan su rabaci wannan sana'a ta su wajen habakar zaman lafiya da inganta hadin kai tsakanin dukkanin al'adu da kuma kabilu dake fadin kasar nan.

Jaridar LEGIT.ng ta kuma ruwaito cewa, an cafke wata Mahaukaciya da ke bara dauke da zunzurutun kudi har N200, 000 can jihar Anamra a Kudancin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel