Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata, hotuna

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata, hotuna

A daren ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba, ne jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake birnin tarayya, Abuja.

Jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood sun cika da murna da farinciki a yayin da su ka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa domin nuna goyon bayansu gare shi.

Akwai annashuwa da fara'a a fuskokin jaruman, maza da mata, a hotunan da su ka dauka da shugaba Buhari yayin ziyarar.

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata, hotuna
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin jaruman fina-finan Hausa maza da mata
Asali: Twitter

Masana'antar Kannywood ta dade tana bawa shugaba Buhari goyon baya, don ko a shekarar 2015 bayan Buhari ya lashe zabe, kafin a rantsar da shi, sai da jaruman masana'antar ta Kannywood su ka kai masa ziyara a gidansa da ke Daura.

DUBA WANNAN: An bankado babbar almundahana a hukumar kula da alhazai ta kasa

Daga cikin jarumana da su ka kaiwa shugaba Buhari wannan ziyara akwai; Hamisu Lamido (Iyantama), Daushe, Nura Hussain (Ya sayyadi), Rukayya Dawayya, Fati Nijar, Sadiq M. Sadiq, Aminu Saira, Rabi'u Rikadawa, Fati Shu'uma da wasu da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel