Jam'iyyu 17 sun gabatar da jerin Sunayen 'yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar tarayya

Jam'iyyu 17 sun gabatar da jerin Sunayen 'yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar tarayya

A yayin da sa'o'i 24 kadai ya rage na cikar wa'adin gabatar da sunayen 'yan takarar kujerar shugaban kasa da na majalisar tarayya, jam'iyyu 17 ne kacal cikin 91 suka cika wannan sharadi na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

Shugaban hukumar zaben na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, shine ya bayyana hakan yayin halartar wani taro tare da wata kungiya ta Civil Society Organisations, CSO, cikin babban birnin kasar nan na tarayya a ranar Talatar da ta gabata.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, a halin yanzu jam'iyyu 17 ne kacal suka gabatar da sunayen 'yan takarar su cikin jam'iyyun siyasa 91 dake kasar nan.

Bisa ga tanadi da tsari na jadawalin hukumar zaben ta INEC, ta kayyade ranar 18 ga watan Oktoba a matsayin ranar karshe da bai wa jam'iyyun siyasa na kasar nan a kan su gabatar da sunayen 'yan takarar su na kujerar shugaban kasa da kuma na majalisar tarayya.

Jam'iyyu 17 sun gabatar da jerin Sunayen 'yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar tarayya
Jam'iyyu 17 sun gabatar da jerin Sunayen 'yan takarar Shugaban Kasa da Majalisar tarayya
Asali: Depositphotos

Dangane da sabanin rahoton na cewar majalisar dokoki ta tarayyar kasar nan ta bayar da amincewar ta kan tanadar N242bn domin gudanar da zaben 2019, hukumar ta yi fashin baki kan cewa N189bn kacal majalisar ta bayar da amincewar ta na tanada domin babban zaben na badi.

KARANTA KUMA: Sai an bi diddigin duk wata dukiyar man fetur da ta bata shekaru 18 da suka gabata - Kotun Kolu ga Gwamnatin tarayya

Kazalika Farfesa Yakubu ya bayyana takaicin sa dangane da kawowa yanzu kaso 25 cikin 100 na na kimanin mutane miliyan 84 da hukumar ta yiwa rajista ba su karbi katukan su na zabe ba da adadin su ya kai miliyan 20.

Shugaban hukumar ya bayyana fatansa da kuma sa rai sauran jam'iyyun za su gabatar da sunayen 'yan takarar su kafin cikar wa'adi na sharadi a yau Alhamis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng