Tambuwal ya nada sabbin kantomomin kananan hukumomi

Tambuwal ya nada sabbin kantomomin kananan hukumomi

A yau Laraba ne Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya nada sabbin kantomonin kananan hukumomi 23 a da kuma nadin sabbin masu bashi shawara na musamman.

A jawabin da ya yi a bukin nadin mukamin, gwamnan ya bukaci dukkan wadanda aka yiwa nadin su dage tukuro domin ganin cewar sun gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.

Ya bukaci suyi aiki domin cigaban al'umma kana su tabbatar da cewar sun gina kyakyawar alaka da kungiyoyin addini da na al'umma da masu sarautun gargajiya a jihar.

Tambuwal ya nada sabbin kantomomin kananan hukumomi
Tambuwal ya nada sabbin kantomomin kananan hukumomi
Asali: Twitter

Ya kuma shawarci su da su kasance masu gudanar da ayyukansu da gaskiya da rikon amana.

DUBA WANNAN: Ba mutunci: Mama Taraba ta kwashe dukkan kayan da ta bawa jam'iyyar APC

Gwamnan ya nada kantomomin ne watanni hudu bayan wa'addin mulkin tsaffin ciyamomin kananan hukumomi na jihar ya kare.

Tambuwal ya yi bayyanin cewar an zabe su ne saboda cancantarsu bayan ya nemi shawarar masu ruwa da tsaki a jihar.

Ta ya ke jawabi a madadin kantomomin, Kantoman Sokoto ta Arewa, Alhaji Aminu Ibrahim ya tabbatarwa gwamnan cewar za suyi iya kokarinsu domin ganin su bawa marada kunya.

Kazalika, Tambuwal ya nada sabbin famanan sakatarori biyu; Alhaji Cika Umar da Buhari Ibrahim.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164