Ighalo ya sake zurawa Super Eagles kwallaye a wasan Libya
- Najeriya ta dare saman teburi a rukuni na E na harin zuwa Gasar AFCON
- Super Eagles ta kuma doke Kasar Libya da ci 3-2 a wasan da aka buga jiya
- Yanzu Najeriya za ta kara da Kasar Afrika ta Kudu a wasan ta mai zuwa
Mun ji labari cewa Najeriya ta dare saman tebur a rukunin ta na wasannin da ake bugawa domin zuwa Gasar Nahiyar Afrika na AFCON. A jiya ne da Najeriya ta samu sa’a kan Kasar Libya inda ta sake doke ta da kuma ci 3-2.
‘Dan wasan gaban Najeriya Odion Ighalo shi ne ya zura kwallaye 2 yayin da Ahmad Musa ya ci 1. Tun a minti 14 ne Super Eagles ta zura kwallo a wasan na ta da Libya inda Iwobi da Ahmed Musa da Ighalo su ka yi wani wasa.
Ahmed Musa ne ya ci wa Najeriya kwallo ta 2 bayan Ighalo ya zura masa kwallo. Sai dai a minti na 35 ne Mohamed Zubya ya zurawa Najeriya kwallo da kai inda a minti na 74 kuma Kasar ta Libya ta sake karawa Najeriya.
KU KARANTA: NLC na neman karin albashin Ma'aikata a Najeriya
Bayan Ahmad Benali na kasar Libya ya kai wasan 2-2 ne dai sai kuma ‘Dan kwallon Super Eagles Ighalo ya ceci Najeriya ya ci kwallon sa ta 2. Kafin nan dama dai Ighalo ya zura kwallaye 3 a karawar farko da aka yi da Libya.
A nan gaba ne Najeriya za ta kara da Kasar Afrika ta Kudu a wasan ta mai zuwa. Kasar ta Afrika ta Kudu dai ta tashi wasan ta ne da kasar Seychelles babu wanda yayi nasara inda aka tashi 0-0.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng