Ta’aziyya: Buhari ya kira mahaifin Hauwa Liman a waya don jajanta masa

Ta’aziyya: Buhari ya kira mahaifin Hauwa Liman a waya don jajanta masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira Malam Mohammed Liman, mahaifin jami’ar kiwon lafiya dake aiki da kungiyar bada agaji ta Duniya wanda mayakan Boko Haram suka kasheta, Hauwa Liman a ranar Talata 16 ga watan Oktoba.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda yace babu mutumin dake kaunar a yi masa irin wannan kira, ya kara da cewa gwamnatin tarayya tayi iya kokarinta don ganin ta ceto Hauwa, amma hakan bai yiwu ba.

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamnatin kasar Amurka ta bayyan alhininta da kisan Hauwa Liman

A ranar Litinin 15 ga watan Oktoba ne mayakan Boko Hara dake biyayya ga kungoyar ISIS suka bindige Huawa bayan kwashe kimanin watanni bakwai tana hannunsu tun lokacin da suka saceta a garin Rann dake jahar Borno tare da kawayenta biyu.

Ta’aziyya: Buhari ya kira mahaifin Hauwa Liman a waya don jajanta masa
Ta’aziyya: Buhari ya kira mahaifin Hauwa Liman a waya don jajanta masa
Asali: UGC

“Yau na yi Magana da Mohammed Liman mahaifin Hauwa, jami’ar unguwar zoma dake aiki da kungiyar ICRC, babu mai son a kira shi irin wannan kira, gwamnatin tarayya ya yi iya bakin kokarinta na ganin ta ceto rayuwar Hauwa amma abin bai yiwu ba.

“Hauwa ta sadaukar da rayuwarta wajen taimaka ma wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, kuma mun yi bakin ciki da ta mutu a hannun yan ta’adda, ina mika ta’aziyya ga mahaifinta a madadin al’ummar Najeriya gaba daya.

“Haka nan na kira shugaban ICRC, P Maurer don jajanta masa bisa rashin Hauwa da suka yi, ICRC suna taimakawa sosai a Najeriya, musamman wuraren da ayyukan ta’addanci ya shafa, mun yaba da kokarinsu.” Inji shugaba Buhari.

Daga karshe Buhari yayi fatan wannan rashin ma’aikaciya da ICRC ta yi ba zai hanasu cigaba da gudanar da aikin ceto a Najeriya ba, yayi kira garesu dasu jajirce akan aikin da suke yi duk da abinda ya faru. Sa’annan ya tabbatar ma yan Najeriya da cigaba da tsaron lafiyarsu gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel