2019: Tambuwal da Makarfi sunyi alkawarin marawa Atiku baya

2019: Tambuwal da Makarfi sunyi alkawarin marawa Atiku baya

- Gwamna Aminu Tambuwal da Sanata Ahmed Makarfi sunyi alkawarin aiki tare a Atiku domin ganin ya yi nasarar zama shugaban kasa

- Tambuwal da Makarfi suna daga cikin yan takara 11 da suka fafata da Atiku a zaben fidda gwani na PDP

- Makarfi ya bayyana cewar nasarar Atiku tamkar nasarar jam'iyyar PDP ne saboda haka za su tabbatar ya yi nasara

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi sun amince za su yiwa jam'iyyar PDP ta dan takarar shugabancin kasar jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar domin ganin ya lashe zaben 2019.

Tambuwal da Makarfi suna cikin 'yan takarar shugabancin kasa 11 da suka fafata a zaben fitar da gwani inda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi nasara a babban taron jam'iyyar da akayi a Port Harcourt a ranakun 6 da 7 na watan Oktoba.

2019: Tambuwal da Makarfi sunyi alkawarin marawa Atiku baya
2019: Tambuwal da Makarfi sunyi alkawarin marawa Atiku baya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Kungiyar Dariqa ta bayyana dan takarar shugaban kasa da za ta zaba

Tambuwal ya yi wannan jawabin ne a jiya a Abuja yayin da shugaban kwamitin sulhu na PDP, Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa da Gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa har ma da Darius Ishaku na jihar Taraba suka hallarci taron a Abuja.

A bangarensa, Makarfi ya ce masu neman takarar sun tafi wajen babban taron PDP a matsayin dan takara amma jam'iyyar ne tayi nasara daga baya saboda haka ya dace dukkansu su hadu waje guda su tabbatar jam'iyyar tayi nasara.

Ya ce ya shafe shekaru masu yawa yana alakar siyasa da Atiku kuma zai taimaka masa domin ganin ya lashe zaben zama shugabancin kasa a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164