Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maboyar 'yan Boko Haram, da dama sun mutu

Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maboyar 'yan Boko Haram, da dama sun mutu

A yau, Litinin, ne hukumar sojin sama ta kasa ta bayyana cewar ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama bayan ta yi ruwan bama-bamai a wata maboyar su dake Bogum, a jihar Borno.

A jawabin da hukumar ta fitar ta bakin kakakinta, Ibikunle Daramola, ta ce ta kai harin ne da jiragenta na yaki guda biyu kirar MI-35.

Kazalika ya bayyana cewar mayakan kungiyar da dama sun mutu sakamakon harin saman da su ka kai maboyar ta su.

"A ranar Litinin, 14 ga wata ne dakarun sojin sama su ka kai hari a maboyar mayakan kungiyar Boko dake Bogum a jihar Borno bayan samun bayanan sirri.

Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maboyar 'yan Boko Haram, da dama sun mutu
Sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a maboyar 'yan Boko Haram
Asali: Depositphotos

"Mayakan kungiyar Boko Haram da dama sun mutu tare da lalata maboyar ta su da mu ka kaiwa hari da jiragen mu ma yaki samfurin MI-35," a cewar Daramola.

A wani labarin mai alaka da wannan, juma'a, a ranar juma'a 12 ga watan Oktoba, ne da misalin karfe 5 na yamma, mayakan kungiyar Boko Haram suka kaiwa dakarun sojin Najeriya, runduna ta 118 harin bazata.

DUBA WANNAN: Sulhunta Atiku da Obasanjo: Na yi koyi ne da fadar Allah da sunnar ma'aiki - Sheikh Gumi

A sanarwar da hukumar sojin ta fitar a shafinta na Tuwita, ta bayyana cewar mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne a sansanin sojojin da ke Arege a karamar hukumar Mobarr dake jihar Borno.

Sai dai jaruman dakarun sojin sun yi nasarar dakile harin tare da mayar da kaikayi kan mashekiya. Bayan sojojin sun dakile harin, sun yi nasarar kwace wasu makamai daga wurin 'yan ta'addar da su ka hada da wata motar dakon bindiga tare da lalata wasu motocin biyu. Yanzu haka dakarun sojin na cigaba da farautar mayakan kungiyar Boko Haram da su ka tsere bayan kai harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng