Haramtawa wasu mutane fita daga Najeriya: Atiku ya ga baikon Buhari

Haramtawa wasu mutane fita daga Najeriya: Atiku ya ga baikon Buhari

A cikin satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya saka hannu kan wata doka da ta hana duk wasu mutane da ake tuhuma a kotu da laifin cin hanci da rashawa daga fita daga Najeriya.

Daga cikin mutanen da dokar ta shafa akwai tsofin gwamnoni 13 da ministoci 7, maza da mata.

Shugaba Buhari ya samu goyon bayan kotu kan dacewar dokar dake da lamba 6 a karkashin jerin dokokin da shugaban kasa ke da ikon yin amfani da su idan da bukatar yin hakan.

Sai dai dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya cewar matakin da shugaba Buhari ya dauka tamkar mayar da Najeriya salon mulkin soja ne da shugaba Buhari ya yi a shekarar 1984.

Jawabin da ofishin yakin neman zaben Atiku ya fitar yau, Lahadi, a Abuja, Atiku ya bayyana cewar duk da akwai bukatar hana aiyukan ta'addanci, amma dole a bi tsarin doka a duk abin da gwamnati za ta yi.

Haramtawa wasu mutane fita daga Najeriya: Atiku ya ga baikon Buhari
Atiku da Buhari
Asali: Depositphotos

"Wannan ba tsarin dimokradiyya da girmama dokar kasa ba ne. Bai kamata shugaban kasar da ya yi rantsuwa zai kare kundin tsarin mulki a ce ya aikata haka ba.

"Wani abun haushi ma shine yadda aka saka sunan tsohon alkalin alakalan jihar Enugu, Cif Innocent Umezulike, mutumin da tuni ya dade da mutuwa.

"Tsarin mulkin Najeriya ya bawa kowanne dan kasa 'yancin yin gogayya da bulaguro duk inda ya ke so. Shugaban kasa bashi da ikon daukan wannan mataki ba tare da samun izinin kotu ba," a cewar jawabin.

Tsofin gwamnonin da dokar ta shafa sun hada da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki, na jihar Adamawa, Murtala Nyako, Gabriel Suswan (Benuwe), Rasheed Ladoja (Oyo), Orji Uzor Kalu (Abiya), Danjuma Goje (Gombe), Attahiru Bafarawa (Sokoto), Mu'azu Babangida Aliyu (Niger), Chimaroke Nnamani (Enugu), Sule Lamido (Jigawa), Gbenga Daniel (Ogun) da Ibrahim Shehu Shema (Katsina). Dokar ta shafi tsofin gwamnoni da yanzu haka ke cikin jam'iyyun APC da PDP.

A cikin jerin sunayen akwai tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya).

DUBA WANNAN: Obasanjo ya fara yiwa Atiku kamfen a kasar Indonesia

A cikin tsofin ministoci akwai Nenadi Usman, Jumoke Akinjide, Bashir Yuguda, Bala Mohammed, Abba Moro, Femi Fani Kayode da Ahmadu Fintiri.

Ragowar sun hada da tsohon shugaban sojoji, Alex Badeh, tsohon shugaban sojojin ruwa, A. D. Jibrin, tsohon shugaban sojin sama, Mohammed Dikko Umar, tsohon shugaban rundunar 'yan sanda, Sunday Ehindero, tsohon shugaban sojojin sama, Adesola Amosu, shugaban kamfanin sadarwa na DAAR, Raymond Dokpesi, tsohon mai bawa tsohon shugaba Jonathan shawara a kan harkokin cikin gida, Waripamoei Dudafa, tsohon alkalin alakalan jihar Enugu, Jastis Innocent Umezulike da kuma tsohuwar alkaliyar kotun daukaka kara ta gwamnatin tarayya, Jastis Rita Ofili-Ajumogobia.

Duk a cikin jerin sunayen, akwai tsohon sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP, Olisa Metuh, Cif Jide Omokore, Ricky Tarfa da babban lauya Dele Belgore (SAN).

Da yawa daga cikin mutanen na fuskantar shari'a a kotuna daban-daban.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel