Obasanjo ya fara yiwa Atiku kamfen a kasar Indonesia

Obasanjo ya fara yiwa Atiku kamfen a kasar Indonesia

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce rainin shugaba Buhari ya sa shi kasa sa hannu a kan kudirin kasuwanci na ACfTA

- Obasanjo ya bayyana cewar dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, sai saka hannu a kan yarjejeniyar da zarar ya hau mulki

- Tsohon shugaban kasar ya fadi hakan ne a bainar jama'a yayin gabatar da jawabi a taron hadin gwuiwa tsanaki bankin duniya da IMF

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya kara shugaba Buhari tare da bayyana shi a matsayin mai rauni.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar Obasanjo ya soki Buhari ne a kan batun kin saka hannu da ya yi a kan wata yarjejeniyar kasuwanci ta kasa da kasa.

Obasanjo ya bayyana kin saka hannu da Buhari ya yi a matsayin rauni tare da bayyana cewar dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, zai saka hannu a kan yarjejeniyar da zarar ya hau mulki.

Obasanjo ya fara yiwa Atiku kamfen a kasar Indonesia

Obasanjo
Source: Getty Images

Obasanjo na wadannan kalamai ne a bainar jama'a yayin gabatar da jawabi a wurin wani taron hadin gwuiwa tsakanin bankin duniya da IMF a garin Bali, kasar Indonesia.

"Zamu samu shugaban kasa da zai sa hannu a kan yarjejeniyar, ba zamu yarda da shugabannin da hannun su ke da rauni wajen saka hannu a kan yarjejeniya mai amfani da muhimmaci ba," in ji Obasanjo.

DUBA WANNAN: Buhari ya bukaci ministansa na sadarwa ya yi murabus

A wani labarin mai alaka da wannan, Obasanjo ya musanta zargin da jam'iyyar APC ta yi masa na cewar yanz aiki ta karkashin kasa domin ganin Amurka ta janye batun hana Atiku shiga kasar.

A daya daga cikin labaranta, Legit.ng ta sanar da ku cewar kakakin Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya bayyana cewar tsohon shugaban kasar bashi da niyyar yin cacar baki da jam'iyyar APC a kan zargin da bashi da tushe balle makama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel