2019: 'Yan takarar shugaban kasa 15 na bazata

2019: 'Yan takarar shugaban kasa 15 na bazata

A yayin da hankulan'yan Najeriya ya fi karkata ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a wannan lokaci da zaben 2019 ke matsowa, akwai wasu 'yan siyasa sanannu a yankunansu da suka shiga takarar.

Fitowar wannan 'yan siyasar ya bawa 'yan Najeriya da basu gamsu da 'yan takarar da APC da PDP suka gabatar ba kuma a yau zamu kawo muku yan takarar shugabancin kasar da kuma jam'iyyun da suka tsaya takara a karkashinsu.

2019: 'Yan takarar shugaban kasa 14 na bazata

2019: 'Yan takarar shugaban kasa 14 na bazata
Source: Twitter

1. Donald Duke - Tsohon gwaman jihar Cross Rivers kuma dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) duk da cewa da farko ya yi gwamna ne karkashin jam'iyyar PDP.

Niyyarsa shine ya shawo kan 'yan Najeriya suyi watsi da APC da PDP.

2. Hamza Al-Mustapha - Tsohon dogarin shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha ya lashe tikitin takarar jam'iyyar Peoples Party of Nigeria (PPN) a gangamin jam'iyyar da akayi a Ado Ekiti.

Masu nazarin lamuran siyasa na ganin Al-Mustapha na da farin cikin matasa kuma zai samu kuri'u daga wajen matasa.

3. Obadiah Mailafia - Dr Mailafia shine dan takarar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC). Mailafia shine tsohon mataimakin Babban Bankin Najeriya.

A baya tsohon shugaban kasa Obasanjo ya zabi shi a matsayin dan takarar da zai zaba amma kwatsam kuma sai gashi ya koma ya bawa Atiku Abubakar tabarrakinsa.

DUBA WANNAN: Atiku ya zolaye Buhari a kan nadin ministoci

4. Oby Ezekwesili - Mrs Ezekwesili sananiya ce a siyasar Najeriya, tayi minista har sau biyu a zamanin mulkin PDP sannan tana daya daga cikin jagororin kungiyar neman ceto 'yan matan Chibok wato Bring Back Our Girls Campaign (BBOG).

Ezekwesili ce yar takarar shugabancin kasa na Allied Congress Party of Nigeria (ACPN).

2019: 'Yan takarar shugaban kasa 15 na bazata

2019: 'Yan takarar shugaban kasa 15 na bazata
Source: Twitter

5. Farfesa Kingsley Moghalu - Farfesa Moghalu gogagen lauya ne wanda ya yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya a baya. A yanzu shine dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP).

6. Omoyele Sowore - Mr Sowore ya zama dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC) ba tare da hamayya ba a zaben da aka gudanar a Duplex Plaza, Shangisha, Legas.

Matashin wanda shi ne ya kafa jaridar Sahara Reporters ya dade yana gwagwarmayar ceto 'yan Najeriya daga hannun shugabani wanda basu kishin kasa.

7. Tope Kolade Fasua - Fasua ne dan takarar jam'iyyar Abundant Nigeria Renewal Party (ANRP). Fasua marubuci ne kuma dan kasuwa kuma shine shugban Global Analytics Consulting Limited da ke hedkwata a Abuja.

8. Gbenga Toyosi Olawepo - Olawepo ya yi suna ne lokacin da aka kama shi tare da wasu shugabanin daliban jami'ar Legas inda suke zanga-zanga kan banbancin launin fata a 1989.

Olawepo shine dan takarar jam'iyyar Alliance for New Nigeria (AAN).

9. Olusegun Mimiko - Tsohon gwamnan jihar Ondo shine ya lashe tikitin takarar shugabancin kasa na Zenith Labour Party. Baya ga gwamna da ya yi, Mimiko kuma ya rike mukamin Ministan Gidaje da Raya Birane kuma ya yi kwamishina sau biyo a jihar Ondo.

10. Sunday Chukwu-Eguzolugo - Shine dan takarar shugabancin kasa na Justice Must Prevail Party (JMPP).

Chukwu-Eguzolugo ya kayar da Eze Odioyenma inda ya lashe tikitin takarar jam'iyyar.

11. Hamisu Santuraki - Santuraki shine Ciyaman din jam'iyyar Mega Party of Nigeria (MPN) kuma har ila yau shine dan takarar shugabacin kasa na jam'iyyar.

12. Ayodele Fagbenro-Byron - Fagbenro-Byron mawaki ne kuma shine dan takarar shugabancin kasa na KOWA Party.

13. Eunice Uche Julian Atuejide - Julian Atuejide yar kasuwa ce kuma lauya wadda ta tsinduma cikin siyasa inda ta samu tikikin takarar shugabancin kasa a National Interest Party (NIP).

14. Alister Soyode - Soyede itace yar takarar shugabancin kasa na Yes Party. Ita ce ta kafa BEN TV da ke kasar Ingila.

15. Fidelis Akhahomen - Akhahomen shine dan takarar shugaban kasa na Young Democratic Party (YDP).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel