Obasanjo rikitaccen tsoho ne da bashi da ra'ayin kansa - Kungiyar Arewa

Obasanjo rikitaccen tsoho ne da bashi da ra'ayin kansa - Kungiyar Arewa

- Kungiyar Arewa Consultative Forum ta yi kacaca da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

- Kungiyar ta ce Cif Obasanjo rikattacen tsoho ne wanda bashi da alkibla a harkokinsa

- Kungiyar ta yi wannan tsokacin ne saboda yadda Obasanjo ya canja ra'ayinsa ya goyi bayan Atiku bayan ya kwashe shekaru yana bata shi a idon duniya

Obasanjo rikitaccen tsoho ne da bashi da ra'ayin kansa - Kungiyar Arewa

Obasanjo rikitaccen tsoho ne da bashi da ra'ayin kansa - Kungiyar Arewa
Source: Twitter

Sakatare Janar na Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Mr Anthony Sani ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo rikattacen tsoho ne mara alkibla da ra'ayin kansa.

Sani ya yi wannan tsokaci ne saboda yadda Obasanjo ya canja ra'ayinsa game da goyon bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Ya kara da cewa ba abin mamaki bane Obasanjo ya sake canja ra'ayinsa ya janye goyon bayan da ya bawa Atiku kafin babban zaben shekarar ta 2019.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 6 da ake amfani da goro da ya dace ku sani

Idan ba'a manta ba dai, Cif Obasanjo ya sha nanata cewar saboda halayen Atiku da ya sani, mudin ya goyi bayansa ya zama shugaban kasar Najeriya, tabbas Allah ba zai yafe masa ba.

Sakataren na ACF ya ce da farko Obasanjo ya yaga katinsa na PDP inda ya ce ba zai sake shiga siyasa ba amma daga baya ya kafa wata kungiyar masu cikin kasa kwatsam kuma ya mayar da ita jam'iyyar siyasa na ADC, daga karshe kuma gashi ya bawa Atiku tabarrakinsa.

Sani ya ce Obasanjo dattijo ne a Najeriya kuma ya kamata halayensa su nuna hakan amma abin kunya ne yadda tsohon shugaban kasar bashi a alkibla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel