Ke duniya: Yansanda sun kama dillalan dake sayar da sassan jikin mutum su 16

Ke duniya: Yansanda sun kama dillalan dake sayar da sassan jikin mutum su 16

Rundunar Yansandan jahar Kogi ta sanar da kama wasu miyagun mutane dake ci tare da sayar da naman mutum don yin tsafe tsafe, tare da yin bajakolinsu a babban hedikwatar rundunar Yansandan Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin Yansandan Najeriya, DCP Jimoh Moshood ya bayyana cewa dukkanin mutanen su goma sha shidda an kamasu ne akan laifin sayar da sassan jikin mutum ga manyan mutane a jahar Kogi da garuruwan dake makwabtaka dasu.

KU KAANTA: Farawa da iyawa: Cacar baki da nuna ma juna yatsa ya kaure tsakanin yan takarar shugaban kasa

Bugu da kari kaakakin ya bayyana miyagun mutanen a matsayin wadanda suka kashe wani jami’in dansanda mai mukamin Inspekta, Abdul Alfa, wanda ke aiki a ofishin Yansanda na Ejule.

Ke duniya: Yansanda sun kama dillalan dake sayar da sassan jikin mutum su 16
Makasa
Asali: Twitter

Miyagun mutanen da aka kama sun hada da: bdulahi Ibrahim Ali, Alhaji Shaibu Adamu, Yakubu Hamidu, Ubile Attah, Julius Alhassan, Shehu Haliru, Abdullahi Tijani, Akwu Audu, Alhaji Abdullahi Zakari, Sale Adama, Musa Abdulahi, Yakubu Yahaya, Adama Shagari, Baba Isah, Isaac Alfa, Idoko Benjamin.

“Yakubu Hamidu dan shekara 38 ne shugaban wani gungun matasa dake garin Ankpa, kuma shine shugaban yan sintiri na garin Ankpa, Yakubu tare da yaransa yan sintiri ne suke kasha mutane tare da yanke sassan jikinsu, musamman mazakutarsu, kai, da sauran sassan jikin sai su sayar ga manyan mutane.” Inji shi.

DCP Jimoh yace mutanen sun tabbatar ma yansanda cewa sune suka kashe dansanda Ispekta Abdul Alfa a ranar 28 ga watan Nuwambar shekarar 2017, sa’annan suka yi awon gaba da bindigarsa.

Daga bisani kuma sun bayyana mutane da suke yi ma aiki da suka hada da Abdullahi Ibrahim da Alhaji Shuaibu Adamu, inda suka ce wadannan mutanen suka sayar ma sassan jikin mutanen da suke kashewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel