Barayin mutane sun sace wani da kwallon Najeriya, sun nemi miliyan 10

Barayin mutane sun sace wani da kwallon Najeriya, sun nemi miliyan 10

Wasu gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dan wasan kwallon kafa na kungiyar Lobi Stars FC, Sunday Akleche tare da matarsa, inda suka nemi a basu naira miliyan goma a matsayin kudin fansa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi garkuwa da Sunday tare da matarsa ne a jahar Abia akan hanyarsa ta zuwa Fatakwal da nufin kai matarsa inda take bautar kasa a garin.

KU KARANTA: Tallar Najeriya: Osinbajo zai shilla wata babbar jami’a ta duniya dake kasar Birtaniya

Zuwa yanzu masu garkuwan sun nemi sai an biyasu kudi naira miliyan goma kafin su sako dan kwallon, bayan da fari sun tubure akan lallai sai an basu naira miliiyan hamsin kafin su sake ma’auratan.

Barayin mutane sun sace wani da kwallon Najeriya, sun nemi miliyan 10
Sunday
Asali: UGC

“A yanzu haka muna Ijebu Ode inda muke atisaye, kuma muna cikin alhinin sace dan kwallonmu, abin takaici ne ace matashin dan kwallo kamar Sunday tare da matarsa sun shiga hannun miyagun mutane.

“Danginsa sun bayyana mana barayin sun nemi a basu naira miliyan 50, amma a yanzu sun sauko zuwa miliyan 10, haka zalika yan uwan dan kwallon, sun nemi mu biyashi albashinsa na watanni biyar masu zuwa, ta yadda zasu samu damar biyan kudin.

“Amma a gaskiya da wuya su samu yadda suke so, amma dai gwamnan jahar Benue ya bada umarnin a biya yan wasan kungiyar alawus alawus da suke bi bashi, don haka muna sa ran kudin zai taimaka ma iyalan Sunday ko yaya.” Inji wani jami’in kungiyar Lobi.

Sunday na buga gaba ne a kungiyar Lobi, kuma yana daya daga ciki jigogin yan wasan da suka nuna bajinta, kwarewa tare da jajircewa a kakar wasan da ta gabata, inda kungiyarsu ta lashe kofin zakarun Najeriya na shekarar 2018.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel