Innalillahi wainna ilaihi raji’un: Wani babban jami’in gwamnati kuma na hannun daman Buhari ya rasu
Mun samu rahoton rasuwar shugaban hukumar kulawa da jiragen kasa na Najeriya, NRC, Injiniya Usman Abubakar wanda ya rasu a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba a garin Abuja.
Legit.ng ta ruwaito Usman Abubakar ya kasance dan cikin gida a wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari, sakamakon dukkaninsu sun fito ne daga masarautar Daura, sai dai shi Usman ya fito ne daga karamar hukumar Sandamu ne.
KU KARANTA: Tallar Najeriya: Osinbajo zai shilla wata babbar jami’a ta duniya dake kasar Birtaniya
Ingantaccen majiyoyi sun tabbatar da cewa Usman ya rasu ne a asibitin Turkish bayan wata yar gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita, a yanzu dai za’a gudanar da jana’izarsa a ranar Juma’a da misalign karfe 2:30 bayan sallar Juma’a a babban masallacin Najeriya na kasa dake Abuja.
Usman ne wanda ya fara zama kwamishinan ayyuka a jahar Katsina a shekarar 1987, haka zalika ya taba zama shugaban kamfanin hada takarda ta jabba, shugaban kamfanin fata ta Daura, da wata kamfani mai zaman kanta Interlink.
A shekarar 2016 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Usmana a matsayin shugaban hukumar kula da jiragen kasa na Najeriya saboda kwarewarsa a harkar sufuri, bugu da kari Buhari ya taba nada shi minista a gwamnatinsa na mulkin Soja.
Usman ya mutu ya bar uwargidarsa, Hajiya Rabi Sule Maiyawo da yaya uku, daga cikinsu akwai Lawal Abubakar, Buhari Abubakar da Mustapha Abubakar. Allah ya jikanshi da gafara, Amin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa
Asali: Legit.ng