Ratata: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa, hotuna

Ratata: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa, hotuna

Dakarun rundunar sojin Najeriya, bataliya ta 112, dake aikin tabbatar da da zaman lafiya a jihar Borno, sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram masu yawa a jiya, Alhamis, 11 ga watan Oktoba, 2018.

A wata sanarwa da hukumar sojin Najeriya ta fitar a daren na jiya, ta bayyana cewar dakarun sojin sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram din ne a wani faturu da suka gudanar a tsakanin kwanar Bale da Ajiri da ke jihar ta Borno.

Sojojin sun kai samame yankin ne bayan tabbatar da cewar mayakan kungiyar Boko Haram din na amfani da wurin domin buya duk lokacin da jami'an soji ke farautar su.

Shugaban rundunar sojin, Laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya yabawa kwazon sojojin tare da basu umarnin su kara matsa wa da sintiri a yankin.

Ratata: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa, hotuna
Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa
Asali: Twitter

Ratata: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa, hotuna
Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram
Asali: Twitter

Ratata: Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram ma su yawa, hotuna
Dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram
Asali: Twitter

Sojojin Najeriya na cigaba da samun galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram da su ka dade su na tayar da hankula a yankin arewa maso gabas, musamman jihohin Borno da Yobe.

DUBA WANNAN: Tsohon IG da APC ta hana takara ya jagoranci addu'ar Allah-tsine a hedkwatar jam'iyya

Sai dai duk da wannan nasara da sojojin ke samu, hakan bai hana mayakan kai harin kunar bakin wake ba jifa-jifa a sassan jihar Maiduguri.

Nasarar da sojojin ke samu ce ta saka shugaba Buhari karawa shugabannin hukumomin soji wa'adin rikon mukaman su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng