Bayan ganawa da Atiku, Obasanjo ya fadi yadda za a shawo kan babbar matsalar Najeriya

Bayan ganawa da Atiku, Obasanjo ya fadi yadda za a shawo kan babbar matsalar Najeriya

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen kirkirar aikin yi ga matasa a bangaren noma

- Obasanjo ya ce akwai dumbin aiyuka a kasar nan, musamman a bangaren kasuwancin amfanin gona

- Tun shekarar 1976 Obasanjo ya shiga harkar noma. Gonar sa dake garin Ota jihar Ogun, na daga cikin manyan gonaki a nahiyar Afrika

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen kirkirar aikin yi ga matasa a bangaren noma.

Obasanjo ya bayyana haka ne yau, Alhamis, yayin da yake jawabi a kan maudu'in 'Rashi aiki a Najeriya da hanyoyin magance shi' a jami'ar Obafemi Awolowo dake garin Ile-Ife, a jihar Osun.

Obasanjo ya ce akwai dumbin aiyuka a kasar nan, musamman a bangaren kasuwancin amfanin gona.

"Kasancewa ta dan kasuwa a bangaren noma, na fahimci cewar akwai dumbin damar samun aiki a bangaren noma," a cewar Obasanjo.

Bayan ganawa da Atiku, Obasanjo ya fadi yadda za a shawo kan babbar matsalar Najeriya
Obasanjo
Asali: UGC

Tun shekarar 1976 Obasanjo ya shiga harkar noma. Gonar sa dake garin Ota jihar Ogun, na daga cikin manyan gonaki a nahiyar Afrika dake samar da kayan abinci, dabbobi da tsuntsaye, musamman kaji.

Wata gonar Obasanjo na daga cikin gonaki 16 da jihar Oyo ta rufe bisa laifin kin biyan harajin tsaftar muhalli.

DUBA WANNAN: Atiku da Buhari Danjuma ne da Danjummai - Tsohuwar ministar PDP

Da yake karin haske a kan harkokin noma, Obasanjo ya bayyana cewar har yanzu Najeriya ba ta gano dumbin damar dake cikin harkar noma ba, hakan ya saka gwamnati ba ta yin wani kokari domin karfafawa matasa gwuiwa su shiga harkar.

A nasa jawabin, shugaban jami'ar OAU, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya nuna takaicinsa bisa yadda gwamnatoci a Najeriya suka kasa shawo kan matslar rashin aiki a tsakanin matasa tare da bayyana cewar jami'o'i na yiwa manhajar su gyare-gyare domin magance wannan babbar matsala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng