Sabon gwamna sabon sarki: APC ta yi juyin mulki a majalisar dokokin jahar Ekiti

Sabon gwamna sabon sarki: APC ta yi juyin mulki a majalisar dokokin jahar Ekiti

Wasu daga cikin yayan jam’iyyar APC sun yi gaban kansu wajen yin juyin mulki a majalisar dokokin jahar Ekiti inda suka tsige kaakakin majalisar, Honorabul Kola Oluwawole a zaman majalisar na ranar Alhamis 11 ga watan Oktoba, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga tsige Kaakakin majalisar dokokin, yayan jam’iyyar APC a majalisar sun tsige mataimakin kaakakin majalisar, Sina Animasaun, bugu da kari Sina da Kola yayan jam’iyyar PDP ne.

KU KARANTA: Bidiyon cin hanci: Sarki Muhammadu Sunusi ye nemi a rufa ma Ganduje asiri

Sabon gwamna sabon sarki: APC ta yi juyin mulki a majalisar dokokin jahar Ekiti
Majalisar dokokin jahar Ekiti
Asali: Twitter

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa an samu wannan juyin mulki ne yayin da ake kirga saura kwanakin da basu kai kwanukan sati daya ba da gwamnan jahar Ekiti Ayodele Fayose zai sauka daga kujerar gwamna ya mika mulki ga tsohon ministan Buhari, Kayode Fayemi, wanda ya lashe zaben gwamnan jahar.

Haka zalika rahotannin sun ruwaito da misalign karfe 11 na safiyar Alhamis ne yan majalisa suka yi awon gaba da Kaakakin majalisa Kola, wanda kowa ya sanshi babban yaron gwamna mai barin gado ne.

Tsige Kaakaki Kola da mataimakin Kaakaki Sine ke da wuya, sai yayan majalisar a karkashin jagorancin yayayn jam’iyyar APC suka zabo sabon Kaakakin majalisar ba tare da bata lokaci ba, inda suka nada Adeniran Alagbada a matsayin sabon Kaakaki, da Gboyega Aribisogan a matsayin jagon majalisa.

Abinka da rabo, sabon Kaakakin majalisar bai dade da fadawa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP ba, inda a watan Yuni yayi wannan sauyin sheka tare da ubangidansa a siyasa Yarima Dayo Adeyeye.

Kamar dai yadda muka ruwaito, masana al’amuran siyasar jahar Ekiti na ganin wannan juyin mulki na da dangantaka da sauyin gwamnati da za’a samu game da tafiyar gwamnan jahar Ayo Fayose, inda za’a rantsar da gwamna mai jiran gado, Kayode Fayemi a ranar Talata 16 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel