Zargin cin hanci, Ganduje ya mayar da martani

Zargin cin hanci, Ganduje ya mayar da martani

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da matani kan rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa cewa an samu bidiyo da ke nuna inda yake karban cin hanci.

Jaridar Daily Nigerian ta bada rahoton cewa an kama gwamna a bidiyo yana karban cin hncin Dala milyan biyar $5m hannun yan kwangila.

Gwamnatin jihar Kano ta saki wannan martani ne da safiyar yau Alhamis, 11 ga watan Oktoba, 2018. Jawabin yace:

"An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan rahoton da wata kafar yada labaran yanar gizo ke yadawa cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na da hannu cikin wani abun kunya. Wannan kokarin cin mutunci ne kawai."

"Wannan sharri bai zo mana da mamaki ba a irin wannan lokaci da zabe ke gabatowa. Jihar Kano a matsayin jihar APC kuma jiha mafi yawan kuri’u, dole ne a yi kokarin mata sharri."

"Muna son sanar da cewa babu gaskiya cikin wannan zarge-zargen kuma idan akwai irin wannan bidiyo, ta bogi ce."

Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel