Messi, Ronaldo, da sauran ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi

Messi, Ronaldo, da sauran ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi

Wannan karo mun shiga fagen wasanni ne inda mu ka kawo maku jerin ‘Yan wasan da su ka fi kowane samun kudi da harkar kwallon kafa a Duniya. A jerin dai akwai manyan ‘Yan wasan da ake ji da su a Duniya.

Messi, Ronaldo, da sauran ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi
Messi ne wanda ya fi kowa samun kudi da kwallon kafa a 2018
Asali: UGC

Lionel Messi ne a kan gaba sai kuma Abokin adawar sa watau Cristiano Ronaldo sannan Neymar wanda yanzu yake taka leda a Kungiyar PSG. Ga dai jerin nan kamar yadda Mujallar FORBES ta fitar:

1. Lionel Messi

Babban ‘Dan wasan Duniya Lionel shi ne kan gaba a wannan jeri inda aka ce a bana kurum zai tashi da Dala Miliyan 84. Ban da harkar kwallo, ‘Dan wasan na Barcelona na ya kan yi wa nanyan kamfanonin Duniya talla.

Messi, Ronaldo, da sauran ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi
Cristiano Ronaldo yana cikin ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi
Asali: Getty Images

2. Cristiano Ronaldo

Bayan ‘Dan wasa Lionel Messi na Kasar Argentina sai kuma Ronaldo. Yanzu dai albashin ‘Dan wasan a Juventus a shekara ya haura Dala Miliyan 30 inda yake kuma samun kusan Dala Miliyan 50 ta wasu hanyoyin.

KU KARANTA: Ana sace birai daga Najeriya a sayar a kasashen waje

3. Neymar Jr.

‘Dan wasa Neymar na Kasar Brazil wanda yake wasa a ‘PSG’ zai tashi da Dala Miliyan 73 a bana. Ban da albashin sa, ‘Dan wasan zai kuma tashi da Dala Miliyan 17 wajen tallan da yake yi wa Kamfanoni.

Messi, Ronaldo, da sauran ‘Yan wasan da su ka fi kowa albashi
'Dan wasan Manchester Pogba a wani wasan su kwanaki
Asali: Getty Images

4. Paul Pogba

‘Dan wasan Manchester United na tsakiya Pogba ne can a na 4 a jerin. A wani lokaci ‘Dan wasan ne ya fi kowa tsada a Duniya. Pogba na karbar fam 290,000 a duk mako ban da kudin da yake samu a wasu harkar.

5. Luis Suarez

‘Dan wasan gaban Barcelona Suarez ne ya tike jerin na mu a 5. ‘Dan kwallon na Kasar Uruguay zai tashi da kusan Dala Miliyan 27 a bana. Albashin kawai da yake dauka a Sifen ya kai kusan Dala Miliyan 20 duk shekara.

Sauran manyan ‘Yan kwallon da ke tashi da makudan kudi sun hada da Sergio Aguero, Angel Di Maria, James Rodriguez, Gareth Bale, Oscar Jr., Kylian Mbappe, Thiago Silva, Wayne Rooney da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng