Rundunar Yansandan Najeriya ta garkame wani dan majalisan wakilai

Rundunar Yansandan Najeriya ta garkame wani dan majalisan wakilai

Daga dawowarsu aiki bayan daukan dogon hoto, yayan majalisar wakilan Najeriya sun ja daga da rundunar yansandan Najeriya, inda suka yi barazanar gayyatar babban sufetan yansanda na kasa daya gurfana a gabansu game da kama guda daga cikinsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an rundunar SARS ne suka yi awon gaba da dan majalisa Abubakar Lado mai wakiltar mazabar Gurara/Suleja/Tafa tun kimanin kwanaki hudu da suka gabata, kuma har yanzu ba zance babu amo, babu wanda ya ji duriyarsa.

KU KARANTA: An fallasa wani gwamna daga yankin Arewa da aka kama yana karbar cin hancin dala miliyan 5

Wani dan majalisa daga jam’iyyar PDP dake wakiltar mazabar Enugu,Toby Okechukwu ne ya fara mika bukatar yansanda su sako lado ga majalisar a ranar Laraba, inda ya bayyana ma majalisar cewa Lado na hannun Yansanda tun kwanaki uku da suka gabata sakamakon matsaloli da aka samu a zaben fidda gwani na APC.

Rundunar Yansandan Najeriya ta garkame wani dan majalisan wakilai
Majalisa
Asali: UGC

“Wannan majalisar na sane da gayyatar da yansanda suka yi ma Lado, kuma ba bias ka’ida aka gayyaceshi ba, don haka an saba ma dokokin dake kare alfarmar yan majalisu wanda suka bukaci a sanar da shugaban majalisar kafin a gayyaci wani dan majalisa ko kuma a kama shi.” Inji shi.

Wannan batu na dan majalisa Toby ya gamsar da takwarorinsa, inda suka yi amanna da cewa wannan mataki da yansanda suka dauka ya zamto tamkar cin zarafi ga majalisar gaba daya, don haka suka nemi yansanda su saki Lado.

Baya ga neman sakin Lado, majalisar ta ce za ta gayyaci babban sufetan yansandan Najeriya ya gurfana gabanta domin ya tsatstsage mata bayani game da kamen da jami’an Yansanda suka yi ma Lado, haka zalika tawagar yan majalisu a karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila zasu gana da babban sufetan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel