Atiku da Buhari Danjuma ne da Danjummai - Tsohuwar ministar PDP

Atiku da Buhari Danjuma ne da Danjummai - Tsohuwar ministar PDP

Oby Ezekwesili, 'yar takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ACPN, ta bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ba zai iya kawowa Najeriya canjin da take bukata ba.

Ezekwesili, mai rajin ganin an sako 'yan matan Chibok, ta kara da cewar, Atiku, dan takarar PDP, na daga cikin tsofin 'yan siyasar da kwata-kwata Najeriya ba ta bukata.

"Ba zai iya kawo canjin da muke bukata a Najeriya ba. Tsohon dan siyasa ne, sabbin 'yan siyasa ne zasu iya kai Najeriya ga tudun mun tsira.

"Bama bukatar tsofin 'yan siyasa da suke saka bukatar abokan su 'yan siyasa a sama da ta jama'ar kasa," a cewar Ezekwesili.

Atiku da Buhari Danjuma ne da Danjummai - Tsohuwar ministar PDP
Oby Ezekwesili, Tsohuwar ministar PDP
Asali: UGC

Sannan ta kara da cewar, bai kamata 'yan Najeriya su zabi kowacce daga ciki jam'iyyun APC da PDP ba a zaben shekarar 2019 domin duk kanwar ja ce, a cewar ta.

Da take magana yayin wani shirin, Sunrise Daily, Ezekwesili ta bayyana cewar Atiku da Buhari tamkar Danjuma ne da Danjummai ne domin a cikinsu babu mai iya kawowa Najeriya cigaba, kamar yadda ta fada.

DUBA WANNAN: Muna nan zuwa gare ka - EFCC ta yi albishir ga daya daga cikin attajiran Najeriya

Sannan ta siffanta APC da PDP a matsayin 'yan tagwaye tare da sanar da cewar matsalolin Najeriya ba zau warware matukar daya daga cikinsu mulki.

Ezekwesili ta ce babban albishir dinta ga 'yan Najeriya shine, idan aka zabe ta a matsayin shugabar kasa za ta kawo karshen kashe-kashe a ake yi a fadin kasar nan tare da gudanar da gwamnati don jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel