Hotunan wata mata 'yar shekara 70 da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

Hotunan wata mata 'yar shekara 70 da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

Rage shekaru a tsakanin 'yan kwallo da masu sana'ar fina-finai da ma a tsakankanin 'yan mata masu kwalisa ba wani sabon abu bane a Najeriya, nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.

Sai dai kuma wani abun ban mamaki da ba'a saba gani ba shine yiwuwar mace da hankalin ta ta karawa kanta shekaru, sabanin ragewar kenan.

Hotunan wata mata 'yar shekara 70 da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya
Hotunan wata mata 'yar shekara 70 da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya
Asali: Instagram

Wannan shimfidar dai da mukayi maku ta zama dole ne biyo bayan wasu hotuna da wata mata ta saki a dandalin sada zumuntar zamani na murnar zagayowar ranar haihuwar ta da ta yi ikirarin cewa ta shekara 70 a duniya.

Matar wadda ta dauki kyawawan hotunan, ta na rike ne da balam-balam din roba masu taswirar lambobin 7 da kuma sifili wanda hakan ke nuni da cewa yawan shekarun ta kenan kamar dai yadda akan yi yanzu.

Haka zalika a karkashin hotunan wadanda suka kayatar matuka, matar ta yi dan takaitaccen rubutu inda ta ce tasan ba lallai ne wasu su yadda da ita ba amma dai ita tasan shekarun ta kenan.

Wannan dai ya jawo cecekuce sosai a tsakanin ma'abota kafar sadarwar zamanin inda wasu sukayi ta taya ta murna tare da addu'ar suma suyi irin tsufan ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel