Yadda zabukan jihar Pilato suke gudana a yinin yau, duk da ana rikici

Yadda zabukan jihar Pilato suke gudana a yinin yau, duk da ana rikici

- A halin yanzu ana zaben kananan hukumomi a jihar Filato

- Akwai rahoton kin fitowar mutane gurin yin zaben

- Ana zaben ne kananan hukumomi 13 a cikin 17 dake jihar

Yadda zabukan jihar Pilato suke gudana a yinin yau, duk da ana rikici
Yadda zabukan jihar Pilato suke gudana a yinin yau, duk da ana rikici
Asali: Depositphotos

A ruwaito rashin fitowar mutane gurin zaben kananan hukumomi na jihar Filato. Ana zaben ne a kananan hukumomi 13 cikin 17 dake jihar. Jos ta arewa, Jos ta kudu, Riyom da Barkin-Ladi ne kananan hukumomi da ba a zaben.

Majiyar mu ta samo mana cewa Gwamna Simon Lalong ya hana zaben sauran kananan hukumomin ne don tabbatar da tsaro a jihar.

Mutane basu fito zabe a mazabun Pinkston, Mangu, Bassa, Langtang ta arewa, Langtang ta kudu da Shendam.

DUBA WANNAN: Takarar Atiku da Ike?: An kai Ike Kotu kan batun kadararsa

Kasa da masu kada kuri'a 10 ne aka samu a layi gurin karfe 11:10 na safe a Youth Centre polling unit a Pankshin ta tsakiya. Hakan ne kuma a sauran mazabun domin kuwa jami'an zaben ke ta jiran mutane.

An samu hargitsi a gunduma 6 a Pankshin inda mutane suka ce jami'an zaben sun zo da wasu takardun rubuta sakamakon zabe bayan wanda zasuyi amfani dasu. Gundumomin sun hada da Dopkai, Kangmun, Jibilik, Jibam, Kagu ang jing,

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng