Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa

Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa

- Atiku Abubakar ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba yin wani kasuwanci ba sai kiwon shanu 150

- Atiku ya kalubalanci Buhari da APC da su kawo ayyukan da suka samawa 'yan Nigeria da zasu tattalin arzikin kasar

- Atiku ya samar da wani bankin yan kasuwa wanda ya daga darajar iyalai 45,000 daga talauci zuwa wadatar rayuwa

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu, yana mai cewar shugaban kasar bai taba gudanar da wata harkar kasuwanci ba a rayuwarsa.

A cikin wata sanarwa daga ofishin watsa labarai na dan takarar shugaban kasar, Abubakar ya ce zaben fitar da gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar cikin tsari na gaskiya mai cike da adalci, ya jefa APC cikin rudani da tashin kokonto makomarta a 2019.

Yana mamakin wanda ke zuci-zucin samun shugabanci tsakaninsa da Buhari, yana mai cewa Nigeria ta kasance "a cikin zunubi na kwararar jinin bayin Allah" tun bayan da gwamnatin Buhari ta fara shugabanci karkashin mutumin da "magana ce kawai ya iya amma bai san yadda zai aikata ba."

Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa
Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa
Asali: Twitter

KARANTA WANNAN: EFCC ta kafa kwamiti na musamman don tuhumar Fayose kan badakalar N1.2bn

"A ranar Lahadi, kungiyar yakin zaben shugaban kasa Buhari ta kaddamar da nata harin wanda bai yi wani tasiri ba. A ranar Litinin sakataren watsa labarai na APC ya furzas da nashi gurguntaccen ra'ayin, inda ya ke zargin Atiki da nuna zuci zuci akan shugabantar Nigeria," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta zayyana kyawawan ayyukan da Atiku Abubakar ya cimmawa, tare da kalubalantar Buhari da ya kawo wani aiki guda daya da ya kammala tun hawansa mulki har zuwa yanzu.

"Kadan daga cikin nasarorin da Atiku Abubakar ya samu a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa sun hada da lokacin da ya ke shugabantar majalisar masana'antu masu zaman kansu ta kasa, inda ya sauya fasalin layukan sada zumunta daga na mutane 50,000 zuwa sama da miliyan 100, haka zalika ya samarwa mutane 500,000 aikin yi, tare da daga tattalin arzikin kasar zuwa $27bn," a cewar sanarwar.

Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa
Buhari bai taba yin kasuwanci ba, kullum shanunsa 150 - Atiku ya caccaki shugaban kasa
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

"Tambayarmu ga Buhari shine ayyuka nawa ne shi da APC suka samawa 'yan Nigeria da zasu dogara da kawunansu kuma su daga tattalin arzikin kasar?

"Kullum babu wata magana da APC ko fadar shugaban kasa suke yi da ta wuce Buhari ya mallaki shanu 150, to shi kuwa Atiku Abubakar ya kware wajen samawa mutane aikinyi, musamman da ya budejami'ar Amurka a Nigeria, da ke garin Yola, da kuma wani bankin yan kasuwa wanda ya daga darajar iyalai 45,000 daga talauci zuwa wadatar rayuwa.

"Haka zalika ya samar da kamfanin Rica Gado, wani kamfani da ke harkokin tsuntsayen gida da dabbobi wanda ya rage yawan rikice rikicen makiyaya da manoma ta hanyar samar da wani tsari na kawo dai-daito maimakon a rinka cewa 'yan Nigeria su bayar da filayensu don kiwon dabbobi wanda ke zama silar tashin hankalin da ya hallakar da mutane da dama a Nigeria.

"A nan muna maganar fannin masana'antu masu zaman kansu, bawai shanun Buhari 150 da kulum basa kara yawa ba, haka suke a kowace shekara," a cewar sanarwar.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel