Ali Nuhu ya samu kyautar digirin girmamawa daga jami'ar kasar waje
Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya samu kayautar digirin girmamawa a kan koyar da sana'a da cigaban matasa daga jami'ar ISM Adonai ta kasar Amurka dake da matsuguni a garin Kotono na kasar Benin.
Jami'ar ta karrama Ali Nuhu ne yayin wani bikin yaye dalibai da bayar da digirin girmamawa na zangon karatu na 2017/2018 da aka gudanar a birnin Lome na kasar Togo a ranar Lahadin da ta gabata.
Yayin bikin, magatakardar jami'ar, Adamu Muhammad, ya bayyana cewar aiyukan taimako da tallafawa da Ali Nuhu ke yi ne ya dauki hankalin jami'ar har ta yanke shawarar karrama shi.
A nasa jawabin, Ali Nuhu, ya godewa mahukuntar jami'ar da karramawar da suka yi masa.
"Na ji dadin karramawar da ku ka yi min da digiri da digir-gir a bangaren koyar da sana'a da tallafawa matasa.
"Ina matukar godiya ga jami'ar ISM ta kasar Amurka da kuma dukkan masu yi min fatan alheri.
DUBA WANNAN: Biyu babu: Ba mu san da takarar Tambuwal ta gwamna ba - PDP
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood da suka raka Ali Nuhu wurin karbar kyautar sun hada da Abubakar S. Mohammed, Umar Gombe, Ishak Ahmad da Rashidoo da wasu da dama.
Ko a kwanakin baya sai da jarumi Ali Nuhu ya lashe wata kyauta da gidan talabijin ya bawa jaruman shirin fim na kudu da arewacin Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng