Dattijo 'dan shekara 55 ya murkushe Yarinya 'yar shekara 10 a jihar Neja

Dattijo 'dan shekara 55 ya murkushe Yarinya 'yar shekara 10 a jihar Neja

Wata babbar Kotun Majistire dake zamanta a babban birnin Minna na jihar Neja, ta bayar da umarnin garkame wani Dattijo a gidan kaso, Michael Itang mai shekaru 55 a duniya, bisa laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 10 fyade.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ana zargin wannan Dattijo mai sana'ar Gadi da laifin keta haddi da kuma cin zarafin karamar yarinya.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwochie, ya shaidawa kotun cewa, a ranar Laraba 3 ga watan Oktoban da ya gabata, wata Mata Grace Tanko, wanda gidanta ke bayan babban Asibitin garin Suleja, tayi karar wannan Dattijo da ake zargi zuwa ga hukumar 'yan sanda.

Ikwochie tayi korafin cewa, Michael ya yaudari 'yar ta mai shekaru 10 kacal a duniya zuwa katarar dakinsa inda ya rinka murkushe ta tare da keta mata haddinta na 'ya mace.

Dattijo 'dan shekara 55 ya murkushe Yarinya 'yar shekara 10 a jihar Neja
Dattijo 'dan shekara 55 ya murkushe Yarinya 'yar shekara 10 a jihar Neja
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, Dattijon ya rinka yaudarar wannan Yarinya da kudade tsakanin N20 zuwa N100 a duk lokacin da ya bukaci biyan bukatarsa ta kwazabar da namiji.

KARANTA KUMA: Soja cikin maye ya ci zarafin wata Mai Tireda a garin Abuja bisa Kuskure

Legit.ng ta fahimci cewa, laifin wannan Bawa mai muguwar zuciya ya sabawa sashe na 18 cikin dokokin kiyaye hakkin Yara na jihar Neja da aka kafa tun shekarar 2010.

Yayin zartar da hukuncin sa Alkalin Kotun Nasiru Mu'azu, ya bayar da umarni ci gaba da garkame Itang a gidan Kaso tare da daga sauraron kararsa zuwa ranar 25 ga watan Oktoba kafin ta sake waiwayonsa.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel