2019: Atiku ba shi da wani abu da zai tallata kansa da shi - Sagay

2019: Atiku ba shi da wani abu da zai tallata kansa da shi - Sagay

- Shugaban Kwamitin Yaki da Rashawa na Buhari, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewar Atiku ba zai kai labari ba a 2019

- Farfesa Sagay ya ce Atiku bashi da wata aiki da ya yi a baya da zai tallata kansa da shi sai tatsuniyoyin gizo da koki

- Sagay ya lissafo nasarori da ayyukan da shugaba Muhammdu Buhari ya yi da zai sanya 'yan Najeriya su sake zabensa

Ciyaman din Kwamitin Yaki da Rashawa (PACAC) na Shugaba Buhari, Farfesa Itse Sagay ya ce babu yadda za'a kwatanta shugaba Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku saboda Atiku bashi da wani abu da ya tsinana a baya.

2019: Atiku ba shi da wani abu da zai tallata kansa da shi - Sagay
2019: Atiku ba shi da wani abu da zai tallata kansa da shi - Sagay
Asali: Twitter

A hirar da ya yi da Daily Independent, Sagay ya ce Atiku baya tayar wa Buhari hankali saboda idan aka duba tarihinsa ba shi da wani abin azo-a-gani illa alkawurra da ba a tabbatar idan zai iya cikawa ba.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Ya kara da cewa shugaba Buhari ya kafa tarihi wajen yaki da rashawa, farfado da tattalin arziki, magance matsalar rashin tsaro a Najeriya musamman yaki da Boko Haram da kuma ayyukan more rayuwar al'umma wadda suka inganta rayuwar talakawan Najeriya.

A kan batun sake fasalin rabon arzikin kasa da Atiku ke ikirarin zai yi cikin watanni shida idan an zabe shi shugaban kasa, Atiku ya ce wannan ba shine abinda zai warware matsalolin Najeriya duk da cewar gwamnatin Buhari ta kafa kwamiti karkashin jagorancin Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna domin duba lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel