Yanzu-Yanzu: Ambasadan Najeriya a kasar Girka ya riga mu gidan gaskiya

Yanzu-Yanzu: Ambasadan Najeriya a kasar Girka ya riga mu gidan gaskiya

Labarin da muke samu yanzu da dumin sa na nuni ne cewa tsohon Ambasadan kasar Najeriya a kasar Girka da Ostireliya mai suna Farfesa Oludare Agbi ya riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Sahara Reporters, Agbi wanda kuma dattijo ne sosai dake rike da sarautar gargajiya ta Asiwaju a masarautar Akure, ya mutu ne da safiyar ranar Laraba, 10 ga watan Oktoba.

Yanzu-Yanzu: Ambasadan Najeriya a kasar Girka ya riga mu gidan gaskiya
Yanzu-Yanzu: Ambasadan Najeriya a kasar Girka ya riga mu gidan gaskiya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dalilai 3 da ka iya sa Buhari ya fadi zaben 2019

Legit.ng dai ta samu cewa ya mutu ne bayan yasa fama da gajeruwar rashin lafiya duk kuwa da cewa ba mu tabbatar da ainihin rashin lafiyar da ke damun sa ba.

Wani na kusa da mamacin dai ya tabbatar da mutuwar ta sa amma sai dai bai bayar da cikakken bayani ba game da hakan inda yace sanarwa na nan tafe.

Mun samu cewa ya mutu ne ya na da shekaru 73 a duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel