Daga Kasar Inyamurai PDP za ta tsaida Mataiamakin Shugaban kasa - Obi

Daga Kasar Inyamurai PDP za ta tsaida Mataiamakin Shugaban kasa - Obi

Tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na rikon kwara watau Ben Obi ya bayyana cewa babu dalilin wani sa-in-sa game da inda Jam’iyyar za ta fito da ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a zaben 2019.

Daga Kasar Inyamurai PDP za ta tsaida Mataiamakin Shugaban kasa - Obi
Ana neman wanda zai yi wa Atiku Mataimakin Shugaban kasa
Asali: UGC

Ben Obi ya bayyana cewa tun ba yau ba Jam’iyyar PDP ta zabi a fito da ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa daga Yankin Kudu Maso Gabashin kasar nan a 2019. Obi yace Inyamurai ne za su fito da Mataimakin Shugaban kasa.

Kamar dai yadda aka tsara cewa Shugaban kasa ya fito daga Arewacin Kasar na a Jam’iyyar PDP, haka aka fitar da wannan tsari inji tsohon Sakataren rikon kwarya na Jam’iyyar. Obi yace don haka babu dalilin a tsaya ana wani surutu.

Sanata Ben Obi yake cewa an shirya wannan tsari ne tun lokacin da kwamitin da aka nada a Jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Ike Ekweremadu ta zauna domin fitarwa Jam’iyyar ta PDP yadda za ta kai ga ci a zabe mai zuwa na 2019.

KU KARANTA: Gwamna Yari zai canji kujerar Yariman-Bakura a APC

Bayan PDP ta sha kasa ne a 2015 aka nada Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ike Ekweremadu su zauna su duba yadda Jam’iyyar za tayi hobbasa ta dawo kan mulki, daga ciki aka tsara inda za a fito da ‘Yan takara.

Yarbawa ma dai sun huro wuta cewa su za su tsaya takara da Atiku a PDP a 2019. Yanzu dai tsohon Mataimakin Shugaban kasar ne ya samu tikitin takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP inda zai kara da Shugaba Buhari a badi.

Daga cikin wadanda ake tunani za a ba kujerar Mataimakin Shugaban kasa a PDP akwai Peter Obi; da shi kan shi Sanata Ike Ekweremadu, Osita Chidoka, Chukwuma Soludo da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel