Shekaru 4 ko 8: Al’ummar kudancin Najeriya sun shiga rudani akan zabar Buhari ko Atiku

Shekaru 4 ko 8: Al’ummar kudancin Najeriya sun shiga rudani akan zabar Buhari ko Atiku

Tun bayan nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya samu a zaben fidda na gwani na takarar shugaban kasar Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, jama’an kudancin Najeriya sun shiga ruda kan wanda zasu zaba, Atiku ko Buhari.

Idan za’a tun uwar jam’iyyar APC a kokarinta na ganin ta zarce a mulki ta sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

KU KARANTA: Dambe: Sanata Kabiru Marafa ya musanta kama shi da aka ce DSS sun yi

Ba wai banbance banbance ko akasin haka dake tsakanin jam’iyyar APC da PDP bane ya sanya jama’an kudancin kasar nan shga rudu ba, illa zangon mulki da yan takarkarun zasu yi a kujerar shugaban kasa idan guda ya samu ya nasara, da kuma komawar mulki kudanci.

Kalubalen da yan kudancin kasarnan suke fama da shi shine; Idan Buhari ya zarce shekaru hudu kacal zai kara, sai ya mika kujerar ga wani daga kudancin kasarnan a jam’iyyar APC, amma idan Atiku ya hau mulki sai ya share shekaru takwas kafin mulki ya koma kudancin Najeriya.

Wannan lamari ba karamin lissafi bane a siyasance, musamman yadda aka mayar da mulkin Najeriya karba karba, duba bayan kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2007, Obasanjo ya mika mulki ga marigayi Umaru Musa Yar’adua, wanda ya rasu cikin shekara uku a mulki.

Mutuwar Yar’adua ta sa aka nada mataimakinsa Goodluck Jonatan shugaban kasa inda ya karasa wa’adin gwamnatinsu, amma a shekarar 2011 da yayi kokarin tsayawa takara sai jigogin PDP yan Arewa suka ce basu yarda ba, sai dai dan arewa ya tsaya takara a PDP don ya karashe shekara hudu da suke ganin hakkin Arewacin Najeriya ne, amma Jonathan ya ki, kuma ya lashe zaben 2011.

Wannan kunnen kashi da Jonathan yayi ya sanya shuwagabannin Arewa hade masa kai a yayin zaben 2015, inda suka mara ma Muhammadu Buhari baya ya samu nasarar zama shugaban kasa, don haka yanzu yan kudu na sauraron Buhari ya kammala wa’adinsa ne a shekarar 2023 ya basu mulki, amma idan Atiku ne ya zama shugaban kasa a 2019, ya zama kenan sai sun jira shekarar 2027 su samu mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel