Fayose ya fadawa APC cewa ta daina mafarkin zai shigo Jam’iyyar

Fayose ya fadawa APC cewa ta daina mafarkin zai shigo Jam’iyyar

Gwamnan Jihar Ekiti Mai Girma Ayodele Fayose ya nuna cewa babu abin da zai hada shi da Jam’iyyar APC mai mulki. Gwamnan da wa’adin sa ya kusa karewa yace babu wani abin da zai kai shi a APC.

Fayose ya fadawa APC cewa ta daina mafarkin zai shigo Jam’iyyar
Gwamna Fayose ya ce babu abin da zai kai sa Jam’iyyar APC
Asali: Depositphotos

Ba da dadewa bane dai Gwamnan mai shirin barin gado yayi barazanar ficewa daga Jam’iyyar sa ta PDP. Gwamnan ya nemi yayi wa Jam’iyyar adawar ta sa bore ne tun lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sha kasa a zaben PDP.

Idan ba ku manta ba, Atiku Abubakar ne yayi nasara a zaben tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa na PDP wanda rashin nasarar Aminu Tambuwal yayi wa Gwamnan ciwo. Fayose dai da wasu Gwamnonin Kudu ne su ka bi bayan Tambuwal.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara Yari zai canji Yariman-Bakura a Majalisa

Fayose ya fadawa Jam’iyyar APC dai su daina mafarkin zai sauya-sheka zuwa Jam’iyyar idan ya bar PDP. Gwamnan ya nuna cewa ko ya rasa inda zai je, ba zai koma Jam’iyyar APC ba. Gwamnan yayi wannan jawabi ne dazu a Garin Ado-Ekiti.

Shugaban APC na Jihar Ekiti Paul Omotoso ya nuna cewa sam ba za su karbi Gwamna Ayo Fayose ba. Shi dai Gwamnan yace bata lokaci ne ma a tsaya har ayi batun zai shiga APC inda yace babu abin da zai taba hada sa da Jam’iyyar mai mulki.

A baya kun ji cewa Mai Girma Gwamna Ayodele Peter Fayose wanda yanzu yake shirin barin karagar mulki yana neman Hukumar EFCC ta biya sa kudi a dalilin ci masa zarafi da tayi kwanaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel