EU za ta tallafawa al'ummar Daura da babban sabuwar transforma

EU za ta tallafawa al'ummar Daura da babban sabuwar transforma

- Kungiyar Tarayyar kasashen Turai za tayi hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyi domin inganta lantarki a Daura

- Kungiyoyin za su samar da babban transformer mai karfin 330KVA da zai samar da lantarki a Daura da wasu garuruwa da ke makwabtaka Daurar

- Ciyaman din karamar hukumar Daura, Abba Mato ya mika godiyarsa da dukkan wadanda suka tallafa wajen aikin

Kungiyar Tarayyar Kasashen Turai (EU) da French Development Bank sunyi wata hadin gwiwa domin samar da na'uarar samar da wuta wato Transforma mai karfin 330KVA a karamar hukumar Daura ta jihar Katsina domin inganta samar da wutan lantarki kamar yadda Kamfanin Raba Lantarki na kasa TCN ya bayyana.

EU za ta tallafawa al'ummar Daura da sabuwar transforma
EU za ta tallafawa al'ummar Daura da sabuwar transforma
Asali: Twitter

Wani jami'in kamfanin, Mr Wale Adeyemi ne ya bayar da sanarwan a yau Talata a yayin da ya tafi ziyarar gani da ido a inda ake aikin kafa transformar, ya ce za a maye gurbin karamar transforma mai 110KVA da 330KVA domin inganta samar da wutan lantarki.

DUBA WANNAN: Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Aso Rock

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya, Kungiyar Tarayyar Turai da French Development Bank da ma wasu kamfanoni masu bayar da tallafi ne suka dauki nauyin aikin. Ya ce idan an kammala aikin zai inganta rayuwar mutanen yankin.

Ya ce garuruwan da za su amfana da aikin wutan lantarkin sun hada da Katsina - Daura - Giwa zuwa Tsamiyar Kara da ke jihar Kano. Ya kuma kara da cewar za a kawo ma'aikata nan take domin fara aikin ba tare da bata lokaci ba.

Ciyaman din karamar hukumar Daura, Alhaji Abba Mato ya ce aikin abin yabawa ne kuma ya mika godiyarsa da gwamnatin tarayya da sauran kamfanonin da suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel