2019: Zaban Atiku tamkar dawo da cin hanci da rashawa ne a Najeriya – Lai Muhammed

2019: Zaban Atiku tamkar dawo da cin hanci da rashawa ne a Najeriya – Lai Muhammed

Ministan harkokin watsa labaru an Najeriya, Alhaji Lai Muhammed ya gargadi yan Najeriya da cewa dain har suka zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar tamkar sun dawo da Najeriya cikin zamanin cin hanci da rashawa ne da ya gabata.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba a yayin da ya kai ziyara zuwa babban ofishin kamfanin watsa labaru na Daar, masu gidan talabijin na AIT da gidan rediyon Ray power a Abuja.

KU KARANTA: Murnar zabe: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku

Lai ya kai wannan ziyara ne a karkashin tsarin wayar da yan Najeriya game da watsa labarum kanzon kurege wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar a ranar 11 ga watan Yuli na shekarara 2018.

Da yake amsa tambayoyi daga yan jaridu, Lai yace yana tabbacin yan Najeriya ba zasu yi zaben tumun dare ba a babban zaben 2019, ya kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne kadai zabin alheri ga Najeriya a 2019.

“Zabin dake gaban yan Najeriya a shekarar 2019 shine kodai su koma shekarun baya inda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare ko kuma su yi gaba don samun cigaba mai daurewa abinda shugaba kasa Muhammadu Buhari ya sa a gaba.” Inji shi.

Ya karkare amsa tambayar da cewa: “Ina da tabbacin yan Najeriya zasu zabi abinda ya fi musu alheri, ba zaben tumun dare ba.” Inji Ministan watsa labaru, Lai Muhammed.

Idan za’a tuna a ranar Lahadin da ta gabata ne Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da kuriu 1, 532 yayin da gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya zo na biyu da kuri’u 693.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel