'Yan fashi da Makami sun kar wani Sufeton 'Yan sanda a Kudancin Najeriya

'Yan fashi da Makami sun kar wani Sufeton 'Yan sanda a Kudancin Najeriya

Mun samu wani rahoto na ban al'ajabi dangane da yadda wasu gungun 'yan fashi da makamisuka yiwa wani Sufeton 'yan sanda kwanton bauna, Ebri Ogban, inda suka kar shi har lahira ta hanyar harbi da harsashi na bindiga.

'Yan fashi da Makami sun kar wani Sufeton 'Yan sanda a Kudancin Najeriya
'Yan fashi da Makami sun kar wani Sufeton 'Yan sanda a Kudancin Najeriya
Asali: Depositphotos

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito wannan lamari ya auku ne yayin da jami'in 'dan sandan ke bakin aikin sa kan hanyar Otop Abasi dake babban birnin Calabar na jihar Cross River.

Tsautsay da Hausawa kan ce ba ya wuce ranarsa ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da Sufeton 'Yan sandan ke kan hanyar sa ta komawa gida bayan ya kammala sauke nauyin da rataya a wuyansa na wannan rana.

Kafin aukuwar wannan lamari kamar yadda wani mashaidin sa ya bayyana, Sunday Akpan, ya bayyana cewa hukumar 'yan sandan ta samu korafin gudanar wani ta'addanci na fashi da makami yayin da kafin ta yi gaggawar aika jami'an ta tuni mai aukuwar ta auku.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke wani mai sayar da gurbatacciyar Barasa a jihar

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Irene Ugbo, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari kan jami'in su da 'yan ta'addan suka dadarawa harbi na harsashin bindiga har sau biyu da nan take yace ga garin ku nan.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne dakarun sojin kasa na Najeriya suka yi karan batta da 'yan ta'adda na Boko Haram a jihar Borno dake Arewa maso Gabashin kasar nan.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel