Murnar zabe: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku

Murnar zabe: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku

Wani maatshi mai suna Kamaludden Bashir ya kama hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja a kasa daga garin Zariya na jahar Kaduna don bayyana farin cikinsa da nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP ya samu a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

A ranar Litinin Bashiry ya fara wannan tattaki, inda a ranar Talata 9 ga watan Oktoba ya isa garin Kaduna akan hanyarsa ta zuwa Abuja, inda ya bayyana ma manema labaru cewa burinsa shine ya isa Abuja cikin kwanaki biyar.

KU KARANTA: Turnuku: Dakarun Sojin Najeriya sun yi gaba da gaba da mayakan Boko Haram a Borno

Murnar zabe: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku
Kamal
Asali: Facebook

“Ina matukar farin ciki da nasarar da Atiku ya samu, wannan ne yasa na kama tattakin zuwa Abuja don na tabbatar masa da cewa ina tare da shi dari bisa dari, haka zalika zan wayar da kawunan dubunnan matasa akan wannan turba ta goyon bayan Atiku domin ya kai kasarnan ga gaci.” Inji shi.

Malam Bashir wanda ya fara tattakin daga kwarbai dake garin Zaria da misalin karfe 6:30 na safiyar Litinin tare da amincewar iyayensa, ya ce yana da yakinin Atiku ne kadai zai iya shawon kan matsalolin tsaro, talauci, rashin aiki da matsalar rikicin addini da kabilanci.

Haka zalika Bashir yace ya gamsu da shirin da Atiku yake yi a duk fadin kasarnan , don haka yace; “Na yarda da Atiku shi yasa nake wannan tattaki don goyon bayansa tare da addu’ar Allah ya bashi nasara a zaben 2019, shin mutumin da zai iya yaki da rashawa a Najeriya.”

A cewarsa, a tsakanin tafiyar da yayi daga Zaria zuwa Kaduna yan fashin sun kwace masa abincin da yayi guzuri dasu tare da yan kudaden da ya riko a hannunsa, amma duk da haka ba zai karaya ba har sai ya isa garin Abuja domin ya cika burinsa.

Daga karshe Bashir mai tattaki yayi kira ga sauran matasan Najeriya dasu mara ma Atiku Abubakar baya domin ya kai kasarnan ga tudun mun tsira.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel