Buhari ya rubuta wasika zuwa ga Saraki, ya ki rattaba hannu kan wasu kudiri 15
- A yau ne majalisar dattijai da takwararta ta wakilai suka dawo daga hutun da suka tafi tun ranar 24 ga watan Yuli
- A zaman majalisar dattijai na yau, shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya karanta wasikar shugaba Buhari kan wasu sabbin dokoki 15
- Majalisar ta kafa wani kwamitin da zai duba sabbin dokokin da Buhari ya ki amincewa da su
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da wasika zuwa ga shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yana mai bayyana yanke shawarar kin saka hannu kan wasu sabbin dokoki 15.
Bayan karanta wasikar yayin zaman majalisar na yau, a karo na farko tun bayan tafiya hutu a watan Yuni, majalisar ta kafa kwamitin da zai kara nazarin sabbin dokokin da shugaba Buhari ya ki amincewa da su.
Duk da kasancewar shugaba Buhari ya aike da wasikar ne tun kafin majalisar ta tafi hutu, amma sai yau ne Saraki ya karanta ta a zauren majalisar.
Bayan karanta wasikar ne, shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan, ya nemi Saraki ya kafa kwamitin da zai sake duba sabbin dokokin da Buhari ya ki saka hannu a kansu.
Daga cikin sabbin dokokin da majalisar ke son saka hannu a kan su akwai na kafa wata cibiyar bincike da kirkira, da na kafa hukumar kula da irin noma da wasu da dama.
DUBA WANNAN: Lokuta 5 da Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa da yadda ta kasance
Kazalika shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin majalisar na sake fasalin dokokin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Da yake magana a kan waskiar da Buhari ya aiko, Sanata Lawan ya bukaci majalisar ta yi amfani da nazarin da shugaban kasar ya yi domin sake duba na tsanaki a kansu.
Bayan wannan kalamai na Lawan ne sai Saraki ya yi kuri'a a tsakanin 'yan majalisar, kuma su ka amince da bukatar kafa kwamitin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng