Lokuta 5 da Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa da yadda ta kasance

Lokuta 5 da Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa da yadda ta kasance

A ranar Lahadi ta karshen makon jiya ne PDP ta sanar da cewar Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ne ya yi nasara a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa da jam'iyyar ta yi a garin Fatakwal na jihar Ribas.

Sai dai wannan ba shine karo na farko da Atiku zai yi takarar neman zama shugaban kasar Najeriya ba.

1993: Atiku ya nemi jam'iyyar SDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a lokacin amma bai samu nasarar cin zaben cikin gida ba.

A zaben cikin gida da aka fata a shekarar tsakanin 'yan takara uku; Atiku, Kingibe da Abiola, Atiku ne ya zo na uku kafin daga bisani maigidansa, Marigayi Shehu Musa Yar'adua, ya lallame shi ya goyi bayan Abiola a zagaye na biyu na zaben cikin gida da jam'iyyar SDP ta yi tsakanin Kingibe da Abiola.

Lokuta 5 da Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa da yadda ta kasance
Atiku
Asali: Depositphotos

2007: Bayan sun kammala wa'adin mulkinsu tare da tsohon shugaban kasa Obasanjo, Atiku ya canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ACN inda ya yi takarar shugaban kasa. Sai dai dan takarar jam'iyyar PDP a wancan lokacin, Marigayi Umar Musa Yar'adua, shine wanda aka bayyana a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shekarar.

2010: Bayan rashin da ya yi a zaben shekarar 2007, Atiku ya kara komawa jam'iyyarsa ta PDP kuma ya kara neman jam'iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa.

Sai dai tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kayar da shi a zaben cikin gida na jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: 'Yan takarar 5 da har yanzu basu taya Atiku murnar nasarar da ya samu ba

2014: Bayan al'amura sun kara dagulewa a PDP, Atiku ya canja sheka zuwa jam'iyyar APC.

A jam'iyyar ma ya tsaya takarar shugaban kasa amma ya kare a mataki na uku bayan sanar da sakamakon zaben fitar da dan takara.

2018: Yanzu haka dai Atiku ne dan takarar jam'iyyar PDP da zai buga da shugaba Buhari na jam'iyyar APC a zaben shekarar 2019.

Wasu masu nazarin siyasar Najeriya sun bayyana cewar tabbas Atiku, mai shekru 72 a duniya, zai fito da karfinsa da kuma dukkan kwarewa da dabarunsa na siyasa domin ya kai ga nasara, musamman idan aka yi la'akari cewar mai yiwuwa wannan ce damar sa ta karshe da zai sake neman takarar zama shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel