Assha! Hukumar jami’ar jahar Legas ta sallami lakcarori guda 3 akan neman dalibansu

Assha! Hukumar jami’ar jahar Legas ta sallami lakcarori guda 3 akan neman dalibansu

Jami’ar jahar Legas ta sanar da sallamar wasu malamai guda uku daga tsangayoyin jami’ar daban daban akan laifin neman dalibai mata da suke yi da kuma nuna rashin nagartattun halaye duk da cewa an sha yi musu gargadi, kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito.

Kaakakin jami’ar, Ademola Adekoya ne ya sanar da haka a ranar Talata 9 ga watan Oktoba, inda yace hukumar jami’ar ta dauki wannan mataki ne bayan kammala taron majalisar koli na jami’ar karo na 119 daya gudana a ranar 4 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Barayin mutane sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mata 2 a Kaduna

Sunayen malaman ya hada da Dakta Sukanmi Odubunmi daga tsangayar ilimin tsimi da tanadi, Dakta Ajani Ogunwande daga tsangayar Ilimin kimiyyar sinadarai, sai kuma Dakta Emmanuel Gbeleyi daga tsangayar ilimin sanin jikin mutum.

Kaakakin yace wannan mataki da hukumar jami’ar ta dauka ya nuna cewa ba zata lamunci duk wasu halayen marasa tarbiya ba, musamman halayyar neman dalibai mata da nufin basu sakamako mai kyau tare da yin barazanar basu sakamako mara kyau idan basu bada hadin kai ba.

Bugu da kari Adekoya yace matakin yayi daidai da manufar jami’ar na inganta hanyoyin jin dadin dalibai da na malamansu. Kaakain yace Odubunm da Ogunwande sun gayyaci wasu dalibai mata ne zuwa ofisoshinsu don su rubuta jarabawa bayan sun zakke musu.

“Shi kuma Gbeleyi wasu dalibai mata biyu ne suka kai kararsa ga ofishin tsaro na jami’ar akan cewa ya aike su sayo wata allura, inda ya zakke musu yayin da suka bingire da barci bayan ya tsira musu alluran.” Inji Adekoya.

Haka zalika Kaakakin jami’ar, Adekoya ya tabbatar da matakin karin girma ga malaman jami’ar su arba’in da tara da sauran ma’aikata dari biyu dake aiki a sassa daban daban na asibitin. Sa’annan ya kara da cewa ma’aikatan wucin gadi ashirin da tara sun samu aikin dindindin a jami’ar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel