BBOG: Masu rajin dawo da 'yan matan Chibok zasu mara wa Ezekwesile baya a takarar 2019

BBOG: Masu rajin dawo da 'yan matan Chibok zasu mara wa Ezekwesile baya a takarar 2019

- Zasu sauka daga shugabancin kungiyar don taya ta takara

- Sun kafa kungiyar shekaru hudu da suka wuce a Abuja

- Sun sha gwagwarmaya da gwamnatocin PDP da APC a baya

BBOG: Masu rajin dawo da 'yan matan Chibok zasu mara wa Ezekwesile baya a takarar 2019
BBOG: Masu rajin dawo da 'yan matan Chibok zasu mara wa Ezekwesile baya a takarar 2019
Asali: Twitter

A wani batu mai sosa rai, wanda tun bayan da aka saci 'yan mata daga makarantunsu a dake birnin Chibok, a kudancin jihar Borno, da aka tabbatar Boko Haram ce tayi, kuma ta tabbatar da kanta, cewa bautar dasu tayi, a yau, kungiyar zata sarara.

Kungiyar wadda ke zama a Yuniti Fauntin da ke Abuja, gaban Otal din Nicon, a yau, ta bayyana sarara wa inda shuwagabanninta hudu zasu sauka daga mimbarin rajin kokarin dawo da 'yan matan makaranta da gaban iyayensu.

Shuwagabannin su hudu, sune, Aisha Yesufu, Florence Ozor, Maureen Kabrik and Dudu Bakam, wadanda dasu ne aka kafa kungiyar a 2014, wadda ta jawo hankalin duniya kan matsalar da a baya ba'a dauke ta da muhimmanci ba.

DUBA WANNAN: Yadda Kwankwaso zai koyi siyasa daga Tinubu

Yanzu dai, dukkaninsu, sun sha alwashin bin Madam Oby Ezekwesile, aikin takara da yakin neman zabe a jam'iyyar Allied Congress Party of Nigeria, wadda ta tsayar da ita takarar kujerar shugaban kasa.

Gwamnatin PDP dai, bata iya ceto kowa ba a wancan lokacin, inda tayi shakulatin bangaro da lamarin. Sai da ta APC tazo, sannan ne ta ceto wasu daga matan, amma daki kusan rabi na can a bauta.

Sun kuma zargi wannan gwamnati itama, da kin nuna damuwa kan sabgar yaran da iyayensu, wadanda tuni wasunsu ma sun mutu don bakin ciki.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel