Bashin Albashin da ma'aikata ke bin gwamnatin jihohinsu a cikin watanni 12 na shekarar 2018

Bashin Albashin da ma'aikata ke bin gwamnatin jihohinsu a cikin watanni 12 na shekarar 2018

- Ma'aikatan jihohi 3 na bin gwamnatocin jihohinsu bashin albashin akalla watanni 5

- Jihohin sun hada da Osun, Kogi da Benue

- Ma'aikatan da matsalar ta shafa sun hada da malaman makarantun sakandire, 'yan fansho, ma'aikatan unguwar zoma da kuma ma'aikatan sakatariyar jihohinsu

A bayanin da Legit.ng ta tattara daga rahoton da wani kamfanin sa ido kan harkokin rabon Albashi da kuma nazari kan albashin da gwamnatocin jihohi ke biyan ma'aikatansu, akalla ma'aikatan jihohi Uku ne ke bin gwamnatocinsu bashi albashin watanni 5.

Rahoton wanda kamfanin BudgIT ya wallafa a shafinsa na facebook da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin, ya nuna cewa jihohin Kogi, Osun da Benue ne matsalar rashin biyan albashin ta fi shafa, wadanda ke bin gwamnatocin jihohinsu bashin albashi, fansho da wasu hakkoki na ma'aikata.

Idan muka fara duba batun bashin da ma'aikatan jihar Kogi ke bin gwamnatin jihar, Rahoton ya nuna cewa a malaman makarantun sakandire na bin bashin albashin watanni 13, ma'aikatan unguwar zoma na asibitin jihar na bin bashin albashin watanni 5 yayin da 'yan fansho da ma'aikatan sakatariyar jihar da ke bin bashin watanni 2

KARANTA WANNAN: Atiku Babban barawo ne a Afrika: Manyan badakaloli 5 da ya tafka - Rahoton Amurka

Bashin Albashin da ma'aikata ke bin gwamnatin jihohinsu a cikin watanni 12 na shekarar 2018
Bashin Albashin da ma'aikata ke bin gwamnatin jihohinsu a cikin watanni 12 na shekarar 2018
Asali: Facebook

Malaman makarantun sakandire a jihar Osun, na bin bashin albashin watanni 15, ma'aikatan unguwar zoma na asibitin jihar da 'yan fansho gami da ma'aikatan sakatariyar jihar kowanne na bin bashin albashin watanni 15.

Jihar Benue kuwa, malaman makarantun sakandire na bin bashin albashin watanni 11, ma'aikatan unguwar zoma na asibitin jihar na bin bashin albashin watanni 4 yayin da 'yan fanso suka gaza samun kudinsu na watanni 12; sai ma'aikatan sakatariyar jihar da ke bin bashin watanni 9.

A jihar Bayelsa ma ma'aikata na bin bashin watanni 3 a cikin shekara ta 16, sai jihar Borno ta gaza biyan 'yan fansho kudadensu saboda tantance su da ake kanyi, yayin da har yanzu gwamnatin jihar Ondo ta gaza biyan kaso 20 na cikin albashin watanni 3 na ma'aikatan jihar.

Jihohin Bauchi, Ebonyi, Edo, Enugu, Jigawa, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Legas, Nassarawa, Niger, Ogun, Rivers, Sokoto da kuma jihar Yobe ne kadai suka biya ma'aikatansu albashi ba tare da wani bangare na binsu bashin ko kwabo ba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel