Shari'ar tsohon shugaban NAMA: Kotu ta amince da shaidar damfarar N7b

Shari'ar tsohon shugaban NAMA: Kotu ta amince da shaidar damfarar N7b

- Kotu ta amince ta duba hujjar EFCC kan cuwa-cuwa

- Ana zargin tsohon shugaban NAMA da cin kudin gwamnati

- An dade ana shari'ar ba ci gaba

Shari'ar tsohon shugaban NEMA: Kotu ta amince da shaidar damfarar N7b
Shari'ar tsohon shugaban NEMA: Kotu ta amince da shaidar damfarar N7b
Asali: UGC

A kokarin hukumar hana cin hanci da rashawa ta kasa, karkashin Ibrahim Magu, kotu mai zama a Legas, ta amince ta duba hujjar EFCC a kan shari'ar da ake wa tsohon shugaban hukumar NAMA, Mr. Ibrahim Abdusalami kan wata cuwa-cuwa da ke gaban kotu.

Ita dai EFCC, tana tuhumar shi Mista Ibrahim Abdussalam ne da cuwa-cuwar N6.8b, wadda wai ya wawure tare da mukarrabansa, zargi da suka musanta.

Alkalin kotun, Justice Babs Kuewumi, na nazarin hujjar EFCC, na kudi da aka zuwa a wani asusu a Zenith bank, mai sunan wata Felicia Nnenna Abubakar.

DUBA WANNAN: Yadda Kwankwaso zai koyi siyasa a hannun Tinubu

Hukumar ta EFCC, tace bayan da aka sanya kudin a asusun matar, an koma ana kwasar kudin kamar ba na gwamnati ba, har N6,850,447,609.90 billion. zargi da ya kai har sau 24, su kuma suka musanta.

An dai kamo wasu daga cikin mukarraban, wasunsu kuma har yannzu suna buya, an kuma tafka cuwa-cuwar ne a zamanin mulkin PDP.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel