Ba zan taba goyon bayan Atiku ba idan Buhari na raye– Inji gwamnan jahar Adamawa

Ba zan taba goyon bayan Atiku ba idan Buhari na raye– Inji gwamnan jahar Adamawa

Gwamnan jahar Adamawa, Bindow Jibrilla ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ba duk da cewa jaharsu daya, kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan watsa labaru na jahar, Ahmad Sajoh ne ya sanar da haka a ranar Litinin yayin ganawa da manema labaru a garin Yola na jahar Adamawa, inda yace tsayawa takarar Atiku ba zai sauya muhimmancin da Bindow ke baiwa APC da dan takararta Muhammadu Buhari ba.

KU KARANTA: Jami’ar Karaduwa: Shahararren dan siyasa zai gina jami’a da kwalejin kimiyya a jahar Katsina

Ba zan taba goyon bayan Atiku ba idan Buhari na raye– Inji gwamnan jahar Adamawa
Binow da Buhari
Asali: Depositphotos

“Gwamna Jibrilla gwamnan APC ne wanda yake ma APC aiki, kuma bas hi da wata manufar goyon bayan duk wani dan takara da ya wuce shugaban kasa Muhammadu Buhari, baya goyon bayan wani dan takara wand aba na APC ba.” Inji Sajoh.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka sanar da Jibrilla a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na takarar gwamnan jahar Adamawa a inuwar jam’iyyar APC, bayan ya kada tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu da surukin Buhari, Modi.

Daga karshe kwamishinan yayi kira ga sauran yan takararun da suka fadi zaben cikin gida dasu hada hannu da Bindow a zaben shekarar 2019 don ganin jam’iyyar APC ta kai ga nasara.

Idan za’a tuna a farkon zangon mulkin gwamna Bindow ne aka jiyoshi yana gode ma Atiku Abubakar bisa gudunmuwar da ya bashi a yayin yakin neman zaben 2015, inda yake neman naira milyan dari uku don yakin neman zabe, amma Atiku ya bashi naira miliyan dari biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel