El-Rufai ya karrama wani attajri da ya dauki nauyin daiban jahar Kaduna
Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karrama wani shahararren attajiri mai karfin arziki, kuma surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Muhammad Indimi, inda ya shirya masa waliman karramawa a Kaduna.
Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya shirya ma Indimi wannan walima ne a fadar gwamnatin jahar dake gidan Sir Kashim Ibrahim a ranar Alhamis din data gabata 4 ga watan Oktoba don bayyana godiyar gwamnatin jahar game da kokarinsa na taimakawa gajiyayyu.
KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar
Haka zalika a jawabinsa, Gwamna El-Rufai ya bayyana farin cikinsa da godiyar al’ummar jahar Kaduna gaba daya game da daukan nauyin karatun daliban jahar Kaduna su ashirin a fannoni daban daban a jami’ar International University of Africa dake kasar Sudan.
A kokarinsa na jin jina ma Attajirin, gwamnan jahar Kaduna ya mika masa wata lambar yabo domin gode masa bisa gudunmuwar da yake baiwa jahar Kaduna, musamman a fannin ilimi
Shima a nasa jawabin, Alhaji Muhammed Indimi ya gode ma gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai bisa karramawar da aka yi masa, sa’annan yayi alkawarin kara daukan nauyin karatun dalibai mata daga Kaduna a fannin likitanci.
Muhammed Indimi yace zai dauki nauyin dalibai matan ne domin bada gudunmuwarsa ga cigaban ilimin kata ta hanyar basu damar samun guraben karatu daban daban.
Idan za’a tuna a shekarar data gabata ne yaron Muhammed Indimi, Ahmed Indimi ya auri diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zara Buhari, wanda a yanzu haka rahotanni suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa
Asali: Legit.ng