APC: Mata biyu sun bayar da mamaki a jihar Adamawa, sun lashe takarar kujerar Sanata

APC: Mata biyu sun bayar da mamaki a jihar Adamawa, sun lashe takarar kujerar Sanata

- Wasu mata guda biyu da suka fito neman takarar kujerar Sanata a karkashin jam'iyyar APC a jihar Adamawa sun bawa maza mamaki

- A kwanakin baya ne Sanatan jihar Adamawa ta tsakiya, Abdul-Azeez Nyako, ya canja sheka daga APC zuwa jam'iyyar ADC in da ya zama dan takarar gwamna

- Sanata mai ci, Ahmed MoAllayidi, da ke wakiltar jihar Adamawa ta kudu, ya sake samun tikitin takara ba tare da hamayya ba

Wasu mata guda biyu da suka fito neman takarar kujerar Sanata a karkashin jam'iyyar APC a jihar Adamawa, sun bawa maza mamaki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an zabi Binta Masi Garba, Sanata daya tilo daga arewacin Najeriya, a matsayin 'yar takarar kujerar Sanatan jihar Adamawa ta Arewa a karo na biyu. An zabe ta ba tare da hamayya ba.

APC: Mata biyu sun bayar da mamaki a jihar Adamawa, sun lashe takarar kujerar Sanata
Aisha Dahiru (Binani)
Asali: Twitter

APC: Mata biyu sun bayar da mamaki a jihar Adamawa, sun lashe takarar kujerar Sanata
Binta Masi Garba
Asali: Twitter

Kazalika an zabi fitacciyar 'yar siyasa a jihar Adamawa kuma tsohuwar mamba a majalisar wakilai ta kasa, Aisha Dahiru (Binani) a matsayin 'yar takarar kujerar Sanatan Adamawa ta tsakiya a karkashin jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: 2019: Shugaba Buhari ya saki sabbin zafafan hotunan yakin zabe, duba

A kwanakin baya ne Sanatan jihar Adamawa ta tsakiya, Abdul-Azeez Nyako, ya canja sheka daga APC zuwa jam'iyyar ADC in da ya zama dan takarar gwamna.

Sanata mai ci, Ahmed MoAllayidi, da ke wakiltar jihar Adamawa ta kudu, ya sake samun tikitin takara ba tare da hamayya ba, kamar yadda NAN ta rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel