Yanzu-Yanzu: Atiku na kan gaba a wajen kirga kuri'un 'yan takarar tikitin shugaban kasa na PDP

Yanzu-Yanzu: Atiku na kan gaba a wajen kirga kuri'un 'yan takarar tikitin shugaban kasa na PDP

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu na nuni ne da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ne ke kan gaba yayin da aka soma kirga kuri'un da aka kada na zaben fitar da gwanin jam'iyyar PDP.

Kamar yadda muka samu, Atiku Abubakar din yayiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fintikau da daman shine ake zaton zai lashe zaben.

Legit.ng ta samu cewa duk wanda ya lashe wannan zaben ya kuma samu tikitin takarar PDP to ana sa ran shi ne zai kara da shugaba Buhari na APC a zaben 2019 mai zuwa.

Cikakken rahoto na nan tafe

Asali: Legit.ng

Online view pixel