Soja cikin maye ya ci zarafin wata Mai Tireda a garin Abuja bisa Kuskure

Soja cikin maye ya ci zarafin wata Mai Tireda a garin Abuja bisa Kuskure

Kwanaki kadan da suka gabata mun samu cewa wani karamin ma'aikacin sojan kasa, Anajo Aloygius na barikin Soji ta Mogadishi a babban birnin kasar nan na tarayya, ya amsa laifin sa na cin zarafin wata Mata mai Tireda a kasuwar Nyanya.

Soja cikin maye ya ci zarafin wata Mai Tireda a garin Abuja bisa Kuskure
Soja cikin maye ya ci zarafin wata Mai Tireda a garin Abuja bisa Kuskure
Asali: Depositphotos

Rahotan kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Anajo ya amsa laifin sa na kutufar wannan Mata, Helen Akula, a bisa kuskure cikin maye yayin da ya nufaci kai hannu kan wani abokin aikin sa.

Sai dai Akula ta musanta lafazin soja inda da ta bayyana cewa, ya hayayyako kan ta ne yayin da ya nemi taimakon sa akan mika mata wata kwalba dake karkashin kujerar da yake zaune cikin wata Mashaya.

Akula ta nemi hukumomi masu ruwa da tsaki akan su dubi wannan lamari na cin zarafi da aka yi mata domin ramawa Kura aniyyarta.

KARANTA KUMA: Wani sabon rikici tsakanin al'umma ya salwantar da rayukan Mutane 17 a jihar Kogi

Legit.ng ta fahimci cewa, sojan ya hakikance kan bakansa da cewa, kuskure ya sanya ya kai hannun wannan Mata kasancewar sa cikin maye yayin da ya nufaci kutafar wani abokin aikinsa da sa'insa ta shiga tsakanin su a Mashayar.

Sai dai ko shakka ba bu hukumar barikin Sojin ta sha alwashin gudanar da binciken diddigi kan wannan lamari domin gano ainhin ba'asinsa tare da fitarwa da Akula hakkinta.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel