Rundunar soji ta samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1 a Borno

Rundunar soji ta samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1 a Borno

- Dakarun sojin Nigeria sun samu nasarar dakile wani mummunan hari da mayakan Boko Haram suka yi yukurin kaiwa a Borno

- Boko Haram ta shirya kai harin ta'addancin ne a sansanin 'yan gudu hijira na Ngala da ke cikin jihar

- Dakarun sojin sun kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1

Da misalin karfe 3:30 na safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Oktoba, wasu mayakan Boko Hara, suka yi yunkurin kai wani mummunan hari a sansanin 'yan gudu hijira na Ngala da ke cikin jihar Borno

Sai dai, dakarun sojin kasar na Batakiya ta 3 da ke Gamboru Ngala, sun dakile wannan harin, tare da bude wuta ga mayakan, inda suka samu nasarar kashe 3 daga cikinsu, yayin da sauran suka arce bayan samun raunuka.

Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shelkwatar rundunar soji ta kasa, wanda ta wallafa a shafinta na facebook, inda ta ce dakarun sun kuma bi sahun mayakan Boko Haram din da suka raunata, wanda hakan ya basu nasarar cafke 1 daga ciki.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Gwamnonin PDP sun rantse ba zasu goyi bayan kowanne dan takara ba

Rundunar soji ta samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1 a Borno
Rundunar soji ta samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 3 tare da cafke 1 a Borno
Asali: Facebook

Haka zalika, sanarwar ta ce, hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar TY Buratai ya jinjinawa dakarun da suka dakile wannan harin, tare da bukatarsu akan ci gaba da sa ido don tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a yankunan da sansanonin 'yan gudun hijiran suke.

A baya Legit.ng ta ruwaito maku cewa hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya zargi masu madafun iko da kuma dattawan jihar Jos na kunna wutar rikicin da ta tashi a jihar.

A cewarsa, kalaman dattawan da masu madafun iko ne suka harzuka zukatan matasan da suka hadda rikici a Jos, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama wadanda basu ji ba basu gani ba, wasun su ma matafiya ne da hanya ta bi da su a yankin.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel