Ban karawa: Wanda yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja saboda Buhari a 2015 yace ba zai kara ba

Ban karawa: Wanda yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja saboda Buhari a 2015 yace ba zai kara ba

- Wanda yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja saboda Buhari a 2015 ya yi nadama

- Yace ba zai kara yin wani tattaki ba saboda 'yan siyasa

- Yace 'yan siyasar Najeriya kan su kawai suka sani

A shekarar 2015, jim kadan bayan da aka sanar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da aka gudanar, wani abun da ya dauki hankalin al'umma shine tattakin da wani matashi yayi daga jihar Legas zuwa Abuja.

Ban karawa: Wanda yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja saboda Buhari a 2015 yace ba zai kara ba
Ban karawa: Wanda yayi tattaki daga Legas zuwa Abuja saboda Buhari a 2015 yace ba zai kara ba
Asali: Depositphotos

Matashin mai suna Suleiman Hashim, a lokacin ya ce yana yin tattakin ne domin taya shugaba Buhari murnan lashe zabe da kuma yiwa 'yan Najeriya murna su ma.

Legit.ng ta samu cewa sai da a wata fira da wakilin majiyar na Daily Trust yayi da matashin, Suleiman ya ce yayi dai a shekarar 2015 amma a wannan karon kam ba zai yi ba.

Haka zalika ya bayyana a cikin firrar ta sa inda yace yana so ya taimaka wa yakin zaben na shugaba Buhari amma har yanzu ba'a kira shi ba balle ma a bashi dama.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin shehunnan malaman addinin kiristanci a Najeriya kuma shugaban majami'un darikar 'yan Katolika shiyyar jihar Sokoto, Dakta Mattew Hassan Kukah ya bayyana cewa a duk duniya shi bai taba ganin shugaban kasar da bai san aikin sa ba irin na Najeriya.

Dakta Kuka, wanda yayi wannan ikirarin a ranar Juma'ar da ta gabata, ya kuma bayyana cewa su shugabannin kasa a Najeriya sukan murde doka ne suyi yadda suke so da ita idan dai har suka ga damar yin hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel