Gwamnati na duba yiwuwar yiwa kayan gona masu bukatar sanyi suto-suto 100 a fadin kasar nan

Gwamnati na duba yiwuwar yiwa kayan gona masu bukatar sanyi suto-suto 100 a fadin kasar nan

- Kayan gona masu saurin lalacewa na da daraja sosai

- Suna bukatar kulawa wadda babu yadda masu noma kanyi da asararsu

- Gwamnati zata yi agaji da gidan sanyi

Gwamnati na duba yiwuwar yiwa kayan gona masu bukatar sanyi suto-suto 100 a fadin kasar nan
Gwamnati na duba yiwuwar yiwa kayan gona masu bukatar sanyi suto-suto 100 a fadin kasar nan
Asali: Original

A kokarin gwamnatin Tarayya na dawo da martabar noma da kiwo a tsakanin 'yan Najeriya, kamar yadda yake a baya, kafin a gano main fetur mai kawo kudi cikin sauki, a yanzu gwamnatin ta sha alwashin taimakawa manoma ta hanyoyi da dama.

Sanin kowa ne cewa manoma kayan miya, masu saurin lalacewa, na jawowa manoma da yawa asara, maimakon su sami kasuwar sayar da kayan miyan, sai su bige da busar dasu a rana a kan hanyoyi don neman sauki.

Busar dasu kuma yana rage musu amfani a jika, da ma dadi da kuma kyaun ido, wanda kan hana riba samuwa.

DUBA WANNAN: Zamu daure duk mai hannu a rugujewar bankuna - Ministar Kudi

A yanzu gwamnati ta sha alwashin kafa tashoshin da zata yi amfani dasu don kyautata harkar noman kayan gonar har guda 100 a fadin kasar nan.

An bayyana hakan ne a bikin taron manoma a jihar Legas a bikin Best Food Global, ta bakin Emmanuel Ijewere, a Farmers’ Field Day, wanda Dizengoff suka shirya don manoma a Epe.

Takanolojin da suka kira Green House, zai kuma baiwa manoma damar noma a kowanne yanayi na shekara, zafi, damina ko sanyi, inda zasu iya noman ne a dakuna.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel